Kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ke Lafiya, Jihar Nasarawa, na dakon yanke hukunci kan karar da ke kalubalantar sakamakon zaben 2023 a jihar.
Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Mista David Ombugadu, yana kalubalantar ayyana Gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a 2023.
- Gwamnatin Nasarawa Za Ta Rushe Gine-ginen Da Aka Yi A Kan Magudanar Ruwa
- Cire Tallafi: Majalisar Nasarawa Za Ta Binciki Yadda Aka Karkatar Da Kayan Tallafin Jihar
An dai shirya zaman kotun a ranar Alhamis don kammala karɓar hujjoji da jawaban lauyoyi na ƙarshe daga ɓangaren mai shigar da kara da jam’iyya da kuma wanda ake kara ko tuhuma.
Alkalin da ke jagorantar zaman shari’ar, Mai shari’a Ezekiel Ajayi, ya dage zaman kotun bayan lauyoyin masu kara da wadanda ake kara sun amince da bukatunsu na karshe a rubuce.
Don haka mai shari’ar ya ce kotun za ta tuntubi bangarorin ta hanyar lauyoyinsu kan ranar da za a yanke hukunci.
Tun da farko, Kanu Agabi (SAN), jagoran masu shigar da kara ya shaida wa kotun cewa ya amince da duk hujjojin da ke cikin rubutattun bukatun da aka gabatarwa kotu.
Lauyan mai kara ya bukaci kotun da ta soke zaben Gwamnan Jihar Nasarawa saboda rashin bin dokar zabe tare da bayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.
Agabi ya kuma bayyana cewa babu wata alaka tsakanin kuri’u a na’urar IREV da sakamakon karshe da aka bayyana.
Lauyan mai shigar da kara ya ce dan takarar PDP ne ya fi yawan kuri’un da aka kada a zaben, bisa ga bayanan da ke cikin IREV da bayanan na’urorin BVAS da aka yi amfani da su a rumfunan zabe daban-daban.
A nasu bangaren, lauyoyin hukumar zabe ta INEC, APC, da Gwamna Sule, Mista Isiaka Dikko (SAN), Hassan Liman (SAN) da Messrs Wole Olanikpekun (SAN), sun rubuta bukatarsu ta karshe a rubuce tare da yin kira ga kotun da ta yi watsi da karar don rashin cancantar saurarensu.
Lauyan jam’iyyar APC, Olanikpekun ya kuma yi zargin cewa mai shigar da karar ya yi watsi da na’urar BVAS da kuma bayanan IREV a kotun ba tare da nuna abin da ke kunshe a cikin bayanan ba.
Ya ce mai shigar da karar ya gabatar da bayanan ne kawai a cikin na’urar IREV da BVAS ga kotun ba tare da nuna su ɓaro-ɓaro a kotun ba.
Don haka ya ce wanda ya shigar da karar ya kasa tabbatar da komai don haka ya bukaci kotun da ta yi watsi da karar.