Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau cewa, kasar Sin ta kakaba takunkumi kan wasu kamfanonin masana’antun sojan kasar Amurka guda biyu, wato Lockheed Martin Corp da Northrop Grumman Corporation, saboda hannunsu a sayarwa yankin Taiwan na kasar Sin da makamai.
Mao Ning ta jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin ta kuduri aniyar kiyaye ‘yancin kai da cikakkun yankunanta.
Don haka, bangaren Sin ya bukaci bangaren Amurka, da ya mutunta ka’idar kasar Sin daya tak a duniya da kuma sanarwowin hadin gwiwa guda uku da kasashen Sin da Amurka suka amince a tsakaninsu, da dakatar da sayar da makamai ga yankin Taiwan, da dakatar da mu’amalar soja tsakanin Amurka da Taiwan, da kuma dakatar da baiwa Taiwan makamai, idan kuma ba haka ba, kasar Sin za ta mayar da martanin da ya dace.(Ibrahim)