Farashin masara ya fadi kasa warwas a kasuwar sayar da hatsi da ke garin Jingir na Karamar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato.
Hakan ya faru ne sakamakon fara samun sabuwar masarar da manoma suka girbe daga gonakinsu, suka kuma kai kasuwa domin sayarwa.
Rahotannin sun nuna cewa, zuwan sabuwar masarar kasuwa ya karya farashinta a kasuwar, inda buhu mai cin kilo 100 a yanzu farashinsa ya kai Naira 37,000.
A makon da ya wuce, an kai masara da dama zuwa kasuwar wanda hakan ya nuna raguwar farashin nata matuka, idan aka kwatanta da yadda farashin yake a makwanni biyu da suka gabata a kasuwar.
Bugu da kari, kafin wannan lokaci da muke ciki yanzu, ana sayar da buhu guda na masara a kasuwar kan Naira 65,000 zuwa Naira 70,000, a wasu kasuwannin da ke a jihar.
Har ila yau, wasu daga cikin dilolin masara a jihar, sun nuna jin dadinsu kan yadda farashin nata ya fadi kasa warwas.
A cewarsu, hakan zai kara samawar da masu amfani da masarar sauki bisa la’akari da yanayin da ake ciki na matsin rayuwa. Wani dillalin masara a jihar mai suna Abubakar Abdullahi, ya bayyana jin dadinsa da cewa,“mun gode wa Allah (SWT), bisa faduwar farashin nata a wannan kasuwa, domin kuwa wannan babban ci gaba ne da aka samu.”
Abubakar ya kara da cewa, “mun sayar da buhun sabuwar masara mai kilo 100 kan farashin Naira dubu 37,000, wanda kuma tsohuwarta a baya ake sayar wa kan Naira dubu 50,000.’’
Shi ma wani kwastoma mai sayen masara, mai suna Samuel Yusuf ya bayanna cewa, samar da wannan sabuwar masara ya taimaka matuka da gaske.
Ya ci gaba da cewa, a makwanni biyu da suka wuce, idan ka shigo wannan kasuwa ba za ka samu masarar ba, wanda hakan ya janyo tashin farashin ta matuka gaya.
Kazalika, shi ma wani manomin mai suna Musa Akans, wanda ya kawo tasa masarar wannan kasuwa, domin sayar wa ya sanar da cewa, ya ji dadi kwarai da gaske sakamakon faduwar wannan farashi nata,
Ya kara da cewa, ko kadan ba a son ransa farashin masarar ya kai har Naira dubu 60,000 zuwa 70,000 ba, musamman a wannan yanayi na yadda mutane suke jin jiki.
Har wa yau, wasu masu ruwa da tsaki a kasuwar sun bayyana ra’ayinsu na hasashen cewa, akwai yiwuwar farashin zai iya ci gaba da karyewa, idan manomanta a jihar suka ci gaba da girbe ta.