Kamar yadda aka sani ne, ana tatsar man darbejiya daga jikin bishiyarta, domin gyaran gashin kai da fatar jikin Dan Adam da kuma sarrafa shi don yin magunguna iri daban-daban.
Wannan dalili ne ya sa kasuwar man darbejiya ke ci gaba da fadada ta hanyoyi daba-daban. Ana kuma samun wannan kara fadada ne, sakamakon ci gaba da tatsar man da ake yi daga jikin bishiyar dogon yaro.
Kazalika an kiyasata cewa, a Kasar Indiya ana samar da Irin Darbejiya da ya kai kimanin tan miliyan 3.5 a shekaru da dama da suka wuce, wanda wannan ya kai adadin tan miliyan 7 na mansa da ake tatsa daga jikin bishiyarsa.
Wannan ya kai yawan man nasa da ake samu a kullum a kasuwanni, wanda ake sarrafa shi zuwa magungunan gargajiya. Haka nan, akwai bukatar zuba kudade da dama a matsayin jari a fannin wannan kasuwanci na man darbejiya.
Har ila yau, a fannin sarrafa wannan mai na darbejiya, ana samun matukar riba wadda ta kai daga Naira dubu 40,000 zuwa 45,000 a duk watan duniya.
Sa’annan, masu sarrafa magungunan gargajiya na sayen man darbejiya, domin sarrafa shi zuwa magunguna da dama. Kazalika, guraren da ake kai man darbejiyar don sayarwa sun hada da, masana’antar da ake sarrafa man kanshi na shafawa. A A irin wadannan masana’antu, ana sarrafa wannan man zuwa nau’ikan man shafawa ko sarrafa shi zuwa sabulun wanka da man gashi da kuma man gyaran fatar jiki da sauran makamantansu.
Bugu da kari, ana yin amfani da man darbejiya domin neman lafiyar Dan Adam. Sannan, wadannan masana’antu na sarrafa man darbejiyar zuwa magungunan asibiti. Masana’antun na sarrafa shi zuwa magungunan da ake shafa wa a fatar jiki ko kuma idan an samu rauni ana a yi amfani da shi ko kuma amfani da shi wajen yakar kwayoyin cuta da ke shafar jikin Bil Adama.
Masana’antun da ke sarrafa man darbejiya, domin kula da fatar Jiki, irin wadannan masana’antun sun kware kwarai da gaske wajen sarrafa man darbejiya zuwa man shafawa a fatar jikin mutum. Haka nan, ana yin maganin amosanin kai da shi da sauransu.
Cibiyoyin kiwon lafiya da ke warkar da ciwon Bil Adama. Ana da wadannan cibiyoyi da ke warkar da cututtuka ta hanyar yin amfani da man darbejiya da kuma yi wa marasa lafiya tausa a jikinsu, don magance tsamin jiki.
Har ila yau, masana’antun aikin gona na sarrafa man darbejiya zuwa magungunan kashe kwari, wadnda ke yi wa amfanin gona illa da kuma kare jijiyoyin shuka daga harbin gansakuka da sauransu.