A jiya ne, aka sanya tsoffin filayen dazuzzukan shayi na tsaunin Jingmai dake Pu’er a kudu maso yammacin kasar Sin, a cikin jerin sunayen kayayyakin tarihi na hukumar kula da ilimi, kimiyya, da al’adu ta MDD (UNESCO).
A yayin taron da aka tsawaita karo na 45 da ke gudana a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, kwamitin kula da kayayyakin tarihi na UNESCO, ya yi nazari kan wurin da kasar Sin ta gabatar, tare da sanya shi cikin jerin sunayen kayayyakin tarihi, wanda ya sanya shi zama wurin tarihi na 57 na duniya a kasar Sin.
Shawarar zabar wurin, ta sanar da babban kuzarin da ya wanzu a yau na tsoffin dazuzzukan shayi da yanayin al’adu masu alaka a tsaunin Jingmai na gundumar Lancang ta kabilar Lahu mai cin gashin kanta dake kudu maso yammacin lardin Yunnan, a matsayin daya daga cikin yankunan da suka fara amfani da albarkatun shayi, kuma suke da tasiri matuka kan al’adun shayi na duniya.
Shinfidar wurin da ya kunshi manyan dazuzzukan shayi guda biyar masu inganci, da kauyukan gargajiya guda 9 a cikinsu, da dazuzzuka guda uku da aka kare a tsakanin su, ta yi fice a matsayin abin misali mai dimbin al’adun shayin da suka ta’allaka kan yadda ake kiyaye tsoffin al’adun noma da gandun shayi.
Shugaban hukumar kula da al’adun gargajiya ta kasar Sin Li Qun, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua yayin tsawaita zaman taron na UNESCO cewa, sanya wannan wuri, ya nuna muhimmancin matsayin kasar Sin a fannin asali, da yadda ake shuka, da cinikayyar shayi, gami da yada al’adun shayi a fadin duniya. (Ibrahim)