• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Daɗe Ana Yi Sai Gaskiya

by CMG Hausa
2 years ago
Gaskiya

Shekarar 2023 ta cika shekaru 20 da kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da ƙungiyar ASEAN wato ƙungiyar ƙasashen kudu maso gabashin Asiya, da kuma cika shekaru 20 da kafuwar baje kolin Sin da ASEAN. Wannan ya ba da muhimmiyar ma’ana ga bikin baje kolin Sin da ASEAN na bana, wanda aka bude a ranar 17 ga watan Satumba a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta ta kudancin ƙasar Sin. 

 

Ƙasar Sin ta ci gaba da rike matsayinta na babbar abokiyar hulɗar kasuwanci ta ASEAN tsawon shekaru 14 a jere, kuma ɓangarorin biyu sun kasance manyan abokan harkalla a fannin cinikayya mafi girma cikin shekaru uku a jere tun daga shekarar 2020. An kara inganta aikin gina yankin cinikayya maras shinge na ƙasar Sin da ASEAN, tare da ƙara ƙarfafa matsayin Sin da ASEAN a matsayin manyan abokan cinikayyar juna. A cikin ’yan shekarun nan, ƙasar Sin ta zama muhimmiyar ƙasa mai saka hannun jari a ƙasashen waje ga ƙasashen ASEAN.

  • An Bude Taron Wakilai Na 8 Na Gamayyar Kungiyar Masu Bukata Ta Musamman Ta Sin

An ci gajiyar bikin baje koli na ƙasar Sin da ASEAN da kuma taron kolin harkokin kasuwanci, haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin ƙasashen ASEAN da ƙasar Sin sun haɓaka daga ingantacciyar cinikayya da zuba jari zuwa haɗin gwiwar ƙarfin samar da kayayyaki na ƙasa da ƙasa, da harkokin kuɗi, da tattalin arziki na fasahar zamani ko dijital, da kiwon lafiya, da yawon buɗe ido, da ilimi da dai sauransu. Haɗin gwiwar dake tsakanin ɓangarorin biyu na da matuƙar tasiri.

 

LABARAI MASU NASABA

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Baje kolin ya ba da dama ga kasashen ASEAN don faɗaɗa fitar da kayayyaki masu inganci da fa’ida zuwa ƙasar Sin, da faɗaɗa cinikayya ta hanyar buɗe sabbin kasuwanni. Kana, zai taimaka wajen ba da gudummawa ga daidaiton ci gaban cinikayya tsakanin Sin da ASEAN.

 

Baje kolin bana ya zama wani abin ƙarfafa gwiwa ga gina yankin cinikayya maras shinge na Sin da ASEAN (FTA). A bukukuwan baje koli na ƙasar Sin da ASEAN na shekarun da suka gabata, an kiyasta cewa ‘yan kasuwa fiye da miliyan 1.1 ne suka halarci bukukuwan baje kolin a jimlance. Ana sa ran baje kolin bana wanda shi ne karo na 20 zai samu halartar ƙasashe fiye da 40 da kuma masu baje koli kusan 1,700.

 

Ga ƙasashen ASEAN, bikin baje kolin wani muhimmin al’amari ne na bunƙasa harkokin cinikayya, zuba jari, da musayar kayayyaki da yawon buɗe ido, wanda zai taimaka wajen ƙarfafa hulɗar tattalin arziki da cinikayya tsakanin ƙasashen Asiya da Sin da sauran ƙasashen yankin, da ƙara yin la’akari da damar da aka samu da aiwatar da yankin cinikayya maras shinge na ƙasar Sin da ASEAN.

 

A bana, masu baje koli kusan 640 daga ƙasashen ASEAN za su baje kolin hajojinsu da suka hada da biscuits, kofi, koko da cakulan da aka yi a ASEAN, da ruwan ‘ya’yan itace ko lemo, da kayan marmari da sauran abinci na musamman. kaza lika, za a yi nune-nunen tufafin sakawa, kayan ado irin su sarka, awarwaro, da ababe masu inganta lafiya da kyawun jiki, da sauran kayayyaki na musamman daga ƙasashen ASEAN.

 

Kamfanoni 120 na Vietnam za su baje kolin kayayyakin gona, da kayan ruwa, da abinci da aka sarrafa, da kayayyakin amfanin gida, yadi da tufafi, da kayayyakin ƙawata gida da aka kera da katako kaman kujeru da gadaje da dai sauransu. Kamfanonin Singapore 23 ne za su halarci baje kolin kuma za su gudanar da ayyukan zuba jari da ci gaban kasuwanci sama da 70.

 

A gefen bikin baje kolin, za a gudanar da taron baje kolin hadin gwiwar zuba jari, da taron zuba jari na masana’antu na ASEAN, da taron daidaita ayyuka, wani taron musamman kan zuba hannun jari a Sin wato “Invest in China Year–Enter Guangxi” a Turance, da dai sauransu, wadannan tarukan za su gudana ne don zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki, cinikayya da zuba jari tsakanin Sin da ƙasashen ASEAN. (Yahaya)

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya
Daga Birnin Sin

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103
Daga Birnin Sin

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Next Post

Babu Adawa Tsakanina Da Messi - Cewar Ronaldo

LABARAI MASU NASABA

Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.