Wasu gungun ‘yan daban da ba a san ko su waye ba sun yi yunkurin kona Majalisar Dokokin Jihar Bauchi a daren ranar Lahadi.
Mai bai wa gwamnan Jihar Bauchi shawarori kan harkokin majalisar jiha da ta tarayya, Hon. Sani Mohammed Burra, ne ya shaida hakan a hirarsa ta wayar tarho da ‘yan jarida a ranar Litinin.
- Eriksen Ya Amince Da Komawa Manchester United
- ‘Yan APC Dubu 5,000 Sun Sauya Sheƙa Zuwa PDP A Katsina
Ya ce, bisa wannan yunkurin wasu bata garin ne ya sanya jami’an tsaro suka rufe Majalisar Dokokin tabbatar da doka da oda.
Burra, ya ce ba a tsige Kakakin Majalisar Dokokin ba zuwa yanzu sabanin jita-jitar da wasu ke yadawa. Sai dai ya ce suna ta kan kokarin shawo kan matsalar cikin gida da ya kunno kai a Majalisar.
Wakilinmu ya ziyarci kakakin ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, domin jin karin bayani kan halin da ake ciki sai dai ya ki cewa uffan kan lamarin.
Wakilinmu da ya ziyarci majalisar a ranar Litinin, inda ya iske an jibge jami’an tsaro sun rufe dukkanin mashigar majalisar sai dai ya ga wasu tayun da aka kona a mashigar majalisar.
Wannan matakin dai na zuwa ne bayan yunkurin wasu ‘yan majalisar dokokin Jihar su 22 na tsige kakakin majalisar Abubakar Y Sulaiman da sauran shugabannin Majalisar.
Idan za a tunawa dai ‘yan majalisar dokokin Jihar 22 sun kada kuri’ar rashin kwarin guiwar su kan salon jagorancin Majalisar, inda suka nemi shugabanninsu da su yi murabus ko su tsigesu.
Ya zuwa yanzu dai majalisar na rufe a karkashin kulawar jami’an tsaron ‘yan sanda da wasu sauran jami’an tsaro.