Ma’ikatar kula da aikin hajji ta Saudiyya ta kebe wa Nijeriya Kujerun aikin hajji guda 95,000 a aikin haji na shekarar 2024.
An sanar da hakan ne, a wata tattaunawar yanar gizo a tsakanin hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON da ma’ikatar kula da aikin hajji da Umrah ta Saudiyya.
A cikin sanarwar da aka fitar a jiya Talata, mahukuntan Saudiyya sun umarci Nijeriya ta kammala dukkan shirye-shirye da kuma tuntuntubar masu kula da ciyar da maniyyata da kula da masaukan su da kuma jigilarsu a cikin kwanuka 120.
Jagoran tawagar Saudiyya Dakta Badr Mohammed Al- Somi, ya yi kira ga hukumar NAHCON ta yi kokari wajen cimma wannan wa’adin a cikin lokacin don hakan ya baiwa ma’ikatar kula da aikin hajji ta Saudiyya ta samun isassen yin shirye-shiryen ta, don a gujewa sake mai-maita matsalar da ta auku a lokacin aikin hajjin 2023.
Tun a farko, a na sa jawabin, shugaban NAHCON Zikrullah Hassan ya yi kira ga mahukuntan Saudiyya su kara kaimi kan maganar kudaden ciyar da mahajjatan da suka sauke faralinsu na aikin hajjin da ya gabata.
Kazalika, ya yi kira ga ma’aikatar kula da aikin hajji ta Saudiyya da ta yi nazari kan adadin kamfanonin da za su yi jigilar maniyyatan daga 10 zuwa 100.