Kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan jihar Bauchi a ranar Laraba ta tabbatar da gwamna Bala Mohammed na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan jihar da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris din 2023.
Idan za a tuna dai a zaben da ya gudana INEC ta sanar da cewa Bala Mohammed na PDP ya samu kuri’u 525,280 yayin da babban abokin karawarsa Sadique Baba Abubakar na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 432,272.
A bisa wannan ne Sadique ya garzaya kotu domin kalubalantar nasarar Bala Mohammed.
Kotun sauraron kararrakin zaben mai alkalai uku karkashin Mai Shari’a P.T Kwahar, ya ce mai korafin ya kasa tabbatar da zarge-zargen da yake yi na cewa an yi magudi a zaben.
Kwahar ya ce, shaidun da mai korafin ya kawo sun ginu ne kawai a kan jita-jita domin ba su san ma rumfunan zaben da suke bayar da shaida a kansu.
Ya ce, hakan ya gaza tabbatar da cewa an yi magudi a zaben kamar yadda mai korafin ya ke ikirari.
A cewarsa, “Zaben ranar 18 ga watan Maris, 2023 ya gudana bisa bin dokoki da ka’idojin zabe don haka korafin da ake yi an koreshi.”