Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce, juyin mulki da sojoji ke yi a nahiyar Afirka, ya nuna cewa, Matasa na neman shugabanni masu ‘yanci.
Sai dai kuma nan take Obasanjo ya kara da cewa, ba zai goyi bayan juyin mulki ba duba da irin ilimin da ya samu a hannun tsohon shugaban mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha. Kamar yadda Daily trust ta rahoto.
Ya yi wannan jawabi ne a dakin karatunsa (OOPL) da ke Abeokuta, jihar Ogun, a yayin wani zaman tattaunawa da wata kungiyar matasa mai suna “Afirka ta ‘yan Afirka ce” (A4A), da Reverend Chris Oyakhilome ya kafa ta.
Da yake amsa tambayoyi game da juyin mulkin da aka yi a Afirka, Obasanjo, wanda ya mulki Nijeriya a matsayin shugaban mulkin soja da kuma zababben shugaban kasa a mulkin Dimokuradiyya, ya ce, akwai wasu abubuwa da ke kara karfafa guiwar sojojin da ke juyin mulkin a Nahiyar.
Tun daga shekarar 2020, Nahiyar Afirka ta fuskanci juyin mulki a kasashe bakwai, wanda na baya-bayan nan ya faru a kasar Gabon a watan Agusta.
Akwai jita-jitar juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Kongo a ranar Lahadi, amma gwamnatin Kongo ta musanta hakan.