Hukumar ‘yan sandan Jihar Kano ta gargadi mazauna Kano cewa za a kama wadanda suka karya doka, za kuma su fuskanci fushin hukumar.
Kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba rundunar ‘yan sandan Nijeriya tare da jami’an tsaro na cikin gida damar tabbatar da doka da oda a fadin jiha.
- DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Kori Gwamna Abba Gida-Gida Ta Tabbatar Da Nasarar Gawuna
- Kotun Zaben Kano: Babu Alkali Ko Daya A Cikin Kotu, Ta Yanar Gizo Ake Yanke Hukunci
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ta bukaci Jama’ar jihar da su bayar da goyon bayasu Kamar yadda ake bukata.
Rundunar ta ce tuni aka aike da Jami’an tsaro hadin gwiwa zuwa lungu da sako a fadin Jihar don tabbatar da aiwatar da dokar ta-baci na Sa’o’i 24 don tabbatar da bin doka kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar a wasika mai lamba: K/SEC/H/435/T.1/153 mai kwanan wata 20 ga Satumba, 2023 wanda zai fara aiki daga karfe 6 na yammacin Laraba, 20 ga Satumba zuwa karfe 6 na yammacin Alhamis, 21 ga Satumba, 2023.