Bayan gindaya wa’adin makonni biyu da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya yi ga wadanda ba su biyan harajin kasa (fili), hedikwatar Hukumar Kula da Harkokin filaye ta Abuja (AGIS) ta cika makil yayin da hukumar ke tattara sama da Naira Biliyan daya a kullum.
An rahoto cewa, masu kokarin biyan harajin kasa da ake biyan gwamnati, sun makare ofishin AGIS don kokarin biyan bashin kafin wa’adin da aka gindaya ya cika.
Wike, ya yi barazanar kwace lasisin filin duk wanda ya haura Makonni biyu bai biya bashin da ake bin shi ba.
Daraktan riko na AGIS, Isiaku Ndatsu Alfa, ya bayyana cewa, an samu karuwar biyan kudin kasa tun bayan da Ministan ya yi barazanar kwace lasisin kasar ga wadanda ba su biya bashin ba.
A cewarsa, wasu ‘yan kudade kadan aka tara daga watan Yuni zuwa Yuli amma bayan barazanar da Ministan ya yi a watan Agusta, biyan kudin kasar ya nunku da sauri zuwa Naira Miliyan N500m har zuwa sama da Naira Biliyan daya.
Ya ce, ya zuwa ranar 17 ga watan Satumba, kudaden da aka tattara ya kai Naira Biliyan N1.9bn, kuma ana kyautata zaton adadin zai rubanya nan da karshen wata.