A shekarun baya bayan nan, mahukuntan kasar Amurka na yawaita jaddada kalmar Takara, a lokutan da suke tattauna batun alakar kasar su da Sin, har ma wannan kalma na neman zama tamkar ita ce Jigon” cudanyar sassan biyu.
Matakai daban daban da gwamnatin Amurka ke dauka, sun bayyana a fili yadda wannan kalma ta “Takara” ta shiga bakin kusoshin gwamnatin kasar, inda take wakiltar matakan nuna fin karfi, da kokarin dakile ci gaban Sin, da ma yiwa Sin din matsin lamba ta fannoni mabanbanta.
To sai idan mun lura da matsayin kasashen biyu, abu ne mai kyau su yi takara mai tsafta a bangarori irin su cinikayya da raya fasahohi. Irin wadannan matakai na takara, ya dace su zamo bisa adalci, da kuma sanin ya kamata, kuma ya wajaba a gudanar da su kan tsari bisa dokoki tabbatattu.
Kaza lika, bai dace su zama matakai na watsi da dokokin raya tattalin arziki, da kuma sharuddan cudanyar sassan kasa da kasa ba. Har ila yau, bai dace a yi amfani da irin wadannan matakai wajen murgunawa wasu sassa ba.
Mun ga misalai da dama, dake nuna yadda Amurka karkashin manufar takara, take amfani da karfin ikonta wajen dakile ci gaban wasu kasashe, tare da salwantar da moriyar wasu kasashen, domin cimma nasarar takarar da ta sanya gaba. Hakika wannan dabara ta sabawa ainihin maanar takara mai kyau, maimakon haka, manufofi ne masu alaka da In ban samu ba, to kowa ya rasa da tunani irin na cacar baka.
Sau da dama, mummunar takara daga bangaren Amurka na harzuka bangaren Sin, tare da lahanta moriyar kasar, da sukar manufofin ta musamman ta fuskar siyasa, da ikon mulkin kai, wanda hakan ya yi matukar keta hurumin kaidojin dangantakar kasa da kasa, da lahanta ginshikin cudanya a fannin siyasa tsakanin sassan biyu.
Don haka dai a takaice, maimakon ingiza matakan fito na fito, da rura wutar sabani da wariya, kamata ya yi sassan biyu su mayar da hankali ga bunkasa matakan cimma moriyar juna, da kyautata mutuntaka, da gudanar da takara a fannin inganta jagorancin alumma, da kiyaye moriyar ’yan kasa.
A matsayin Amurka da Sin na kasashe masu karfin tattalin arziki, kamata ya yi takararsu ta karkata ga nunawa duniya kyakkyawan misali, na yadda suke sauke nauyin bunkasa rayuwar alummunsu, da farfado da ci gaba bayan annoba, da shawo kan kalubalen sauyin yanayi, da matsalolin yankunansu, da kare kyakkyawan yanayin muhallin duniya, da wanzar da zaman lafiya, da samar da wadata ga alummun duniya kusan biliyan 8, ciki har da Sinawa da Amurkawa. (Saminu Alhassan)