Alkalin kotun Majistiri da ke Hadejia jihar Jigawa, mai shari’a, Mannir Sarki Jahun, ya yankewa wasu mahaya dawaki biyu hukuncin wata hudu a gidan gyaran hali ko kuma tarar Naira dubu 25 kowannen su.
Kotun tana tuhumar su ne da gudu a doki cikin yanayi mai hadari.
- Yadda Aka Yi Wa Wata Mata Yankan Rago A Hadejia
- ‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutum 5 Da Ake Zargi Da Fashi Da Makami A Jihar Jigawa
Ya ce wadanda ake tuhumar sun amsa laifin da ake tuhumarsu da aikatawa ranar 30 ga watan Agusta 2023.
Ya ce kotun ta yanke hukuncin ne kan takaitacciyar shari’a a karkashin sashe na 123/8 na dokar shari’a.
Dan sanda mai shigar da kara a kotun, Sifeto Christopher Ravel, ya ce wadanda ake tuhumar suna gaban kotu ne bisa zarginsu da hawa doki a lokaci mai hadari a cikin gari.
Sakamakon hakan ya yi sanadin wasu mutane uku sun samu raunika.