Ministan Labarai na Nijeriya, Mohammed Idris Malagi, ya bayyana cewa, Nijeriya na kara kwarjini samun tagomashi da kwarjini a idon duniya karkashin kyakkyawan jagorancin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake bai wa kasar.
Ministan Labaran ya bayyana hakan ne jiya a tattaunawar da ya yi da Gidan Talabijin na Nijeriya (NTA) a Babban Taron Majalisar dinkin Duniya da ake gudanarwa a New York dake Amurka, inda ya kara da cewa, Shugaban Nijeriyar ya kara fito da martabar ba wai kawai Nijeriya ita kadai ba, a’a, har ma da Nahiyar Afrika bakidaya.
- Yadda Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Tsara ‘Yan Nijeriya Da Farfaganda – Atiku
- Zargin Daura Aure Da Mai Kanjamau: Yadda Aka Tube Hakimi A Katsina
“Ziyara ce mai matukar ban sha’awa da Shugaban kasar ya gudanar. Ya zo ne ba don Nijeriya kadai ba, amma har ma da Afrika,” inji shi.
“Tabbas kun gan shi (Shugaba Tinubu) tare da Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramophosa; kun gan shi da Shugaban Tarayyar Comoros, Shugaba Azali Assoumani, kun gan shi tare da Aaki Hussein na Jordan da Shugaban kasar Angola, inda dukkanninsu suka kasance a shirye suke wajen ganin Nijeriya ta daidaita a inda ta dace da matsayinta.
“daga dukkan alamu duniya tana sake maraba da Nijeriya izuwa ga martabar da ta dace da ita. Abubuwa da dama suna ta faruwa.
“Ana sa ido kan Nijeriya don ganin ta yi jagoranci tafiyar, kuma Shugaba Tinubu yana jan ragamar a halin yanzu. Don haka a yanzu Nijeriya tana sake zama muhimmiyar kasa a duniya ta hanyar komawa kan matsayinta da aka san ta da shi.”
Daga nan sai Ministan ya bayar da misali da irin yadda Shugaba Tinubu ya gabatar da tsararre kuma kyakkyawan jawabinsa a gaban Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniyar, inda ya tabbatar da tsarin siyasar dimukradiyya a matsayin tsari mafi inganci dake bayar da cikakken ’yanci da jin dadi da walwala ga al’umma da kuma yadda Afrika ke fama da tashe-tashen hankulan masu tsattsauran ra’ayi a nahiyar ta yadda ta janyo hankalin kasashen duniya, don su kawo agaji a yankin.
Daga nan sai Malagi ya yi wa ’yan Nijeriya albishir kan yadda Tinubu ya samu amincewar Kamfanin EddonMobil, wanda ya yi alkawarin samar da makamashi 40,000 a matsayin sabon zuba jari a kasar.