Yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga taron kolin dandalin tattaunawar neman dauwamammen ci gaba kan aikin sufuri na kasashen duniya.
Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana gaggauta aikin raya harkokin zirga-zirga, domin ta zama kan gaba a wannan fanni a duniya, da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa wajen raya ayyukan sufuri, da kuma samar wa kasashen duniya damammaki a yayin da take neman bunkasuwar kanta. Kaza lika kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasashen duniya, bisa ka’idojin yin mu’amala da juna, da yin hadin gwiwa da juna, da cimma moriyar juna, domin tallafa wa jama’ar kasa da kasa ta hanyar neman dauwamammen ci gaban aikin zirga-zirga. Tana kuma fatan ba da karin gudummawa wajen aiwatar da shawarar bunkasuwar kasashen duniya, da cimma burin neman dauwamammen ci gaba zuwa shekarar 2030 na MDD, da kuma karfafa dunkulewar dukkanin bil Adama.
A yau ne, aka bude taron kolin dandalin tattaunawar neman dauwamammen ci gaba a fannin sufuri na kasashen duniya a birnin Beijing, wanda babban takensa shi ne “Neman dauwamammen ci gaba a aikin sufuri, da hada kai domin raya kasashen duniya”. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)