• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Haifar Da Ambaliya A Libya?

by CGTN Hausa
2 years ago
Libya

A jiya ne agajin jin kai da gwamnatin kasar Sin ta samar ya isa Libya.
Bisa alkaluman da hukumar Libya ta samar a ranar 23 ga wata, an ce, mutanen da ambaliyar ta halaka wadanda aka yi rajistarsu tuni ya kai 3845. Sai dai sakamakon yadda dubban mutanen da suka bace, yawan mutanen da ambaliyar ta halaka a hakika zai zarce adadin da yawan gaske.

Munanan illolin da ambaliyar ta haifar sun kuma sa mutane sun fara tunani game da me ya haifar da wannan mummunar masifa?Wasu sun ce bala’i ne daga indallahi, amma karin mutane na ganin cewa, Amurka da sauran kasashen yamma ne ya kamata su dauki nauyinta.

  • “Mafarkina Na Zuwa Sararin Samaniya” 
  • Sin Tana Bayar Da Babbar Gudummawa Ga Gina Al’ummar Duniya Mai Makomar Bai Daya

Birnin Derna da ke gabashin kasar Libya shi yake fi fuskantar barnar da ambaliyar ke haifarwa, inda ambaliyar ta rushe wasu madatsan ruwa biyu na wurin, lamarin da ya sa ambaliyar ta lalata unguwannin birnin da dama.An ce, madatsan ruwa da suka rushe a sanadin wannan ambaliya tuni suka fara yoyo, kuma mai gudanar da madatsan ruwan da kuma masana suka yi gargadin hadarin da ake iya fuskanta.

A lokacin mulkin Muammar Gaddafi, gwamnatin Libya ta taba cimma wata yarjejeniya tare da wani kamfanin kasar Turkiyya game da gyara madatsan ruwan, amma sakamakon yadda Amurka da sauran kasashen yamma suka hambarar da Libya a shekarar 2011 da sunan wai kare fararen hula daga mulkin Gaddafi, yarjejeniyar ma ta zama banza. Daga nan kuma, Libya ta tsunduma cikin yakin basasa da baraka, lamarin da ya sa aka dakushe karfin kasar, manyan ababen more rayuwa na kasar ma sun lalace, abin da kuma ya rage karfin kasar wajen rigakafin bala’u da ma tinkararsu. Da a ce tsarin hasashen bala’u na kasar na gudana yadda ya kamata, kuma an gyara madatsan ruwan cikin lokaci, da aka kai ga magance mutuwar akasarin mutanen a ambaliyar.

Libya kasa ce da ke da mafi yawan man fetur da aka gano a nahiyar Afirka, wadda ya kamata al’ummarta suka ji dadin rayuwar wadata, amma ga yanayin da suka samu kansu a ciki. Ma iya ce, Amurka da sauran kasashen yamma ne suka jefa su a cikin wannan mawuyacin hali. Kamar yadda wasu masu bibbiyar shafukan sada zumunta suka ce, “Yadda kasashen yamma suka kaddamar da yaki a Libya da ma kakaba mata takunkumi bayan yakin, sun sa wa kasar tarnaki wajen tabbatar da ci gabanta, abin da ya sa kasar da a baya ta kasance tamkar aljanna ta tsumdumma cikin wuta.”

LABARAI MASU NASABA

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

“Ambaliyar da ta afkawa Derna ba safai a kan ga irinta ba a tarihi, duk da haka, kasashen yamma ne suka haifar wa al’ummar Libya wannan mummunar masifa sakamakon yadda suka kutsa cikin kasar.” (Mai Zane:Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26
Daga Birnin Sin

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Next Post
Kimiyya

Masana Kimiyya Na Kasashen Kenya Da Sin Sun Kaddamar Da Kundin Farko Game Da Nau'ikan Tsirran Da Kenya Ta Wallafa

LABARAI MASU NASABA

Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.