A tsakiyar Nijeriya, ana fuskantar wata cutar mai kisa ba tare da bata lokaci ba, cutar kuwa ita ce, cutar mashako, wadda ke bazuwa kamar wutar daji a wasu jihohin Arewacin Nijeriya da suka hada da Borno, Bauchi da kuma Kano.
Tuni kungiyar nan ta Likitoci ta ‘Médecins Sans Frontières (MSF)’ ta ankarar da al’umma tare da bayar da rahoton cewa, dubban yara sun mutu daruruwa ta kuma rasa rayukansu sakamakon cutar.
- CISA: Masana’antun Sarrafa Karfe Na Tafiya Cikin Yanayi Mai Karko Tsakanin Watan Janairu Zuwa Na Agusta
- Babu Wata Yarjejeniya Tsakaninmu Da Gwamnatin Tarayya Kan Dakatar Da Yajin Aiki – NLC
A ra’ayinmu, wannan babbar matsala ce da ke bukatar a gaggauta daukar matakin kawo karshen cutar a matakin kasa da ma duniya baki daya.
Da farko, mun yi tunanin cewa, cutar Mashako, wata cuta ce da aka manta da ita, aka barta a kundin tarihi da ke littatafai, godiya ga shirin rigakafi da aka yi a fadin duniya a shekarun baya. Amma kuma bayyanar ta a ‘yan shekarun nan ya nuna mana bukatar a kara daukar mataki na kariya ga al’ummar mu.
Tawagar Likitocin kungiyar MSF ta bayyana cewa, sun tabbatar da yi wa mutum 6,700 maganin cutar, a yayin da aka tabbatar da barkewar cutar a Kano, an kuma samu bullar cutar har sau 110 a Jihar Borno, a Jihar Bauchi kuma an samu mutum 21 da suka kamu ana kuma ci gaba da sa ido a kan sassan Nijeriya don kare yaduwarta.
Ba zamu manta da bayanin da ke nuna cewa, an samu mutun fiye da 4,000 da suka kamu da cutar a fadin duniya. Wannan kididdigar tana tayar da hankula, tana kuma nuna bukatar a gaggauta daukar mataki don kada abin ya zama annoba.
Cutar na samun karuwar yaduwa ne saboda wasu dalilai masu yawa da suka hada da karancin rigakafi abin da ya sa al’umma da dama suka zama cutar na iya kama su duk kuwa da cewa, cutar aba ce da za a iya daukar matakin kariya daga gareta. Haka kuma karancin maganin rigakafin mai suna ‘Antitodin’ yana kara sanya cutar ta zama abar fargaba ga duk wani mai kishin kasa, wannan kuma shi ne yake kara wahalar da ake fuskanta sakamakon cutar da kuma mace-macen da ake yi.
A ta bakin wani Likita daga kungiyar MSF mai suna Dakta Hashim Juma Omar, lamarin nada tayar da hankali musamman a Jihar Kano. Don kuwa fiye da mutum 700 masu dauke da cutar Mashako na neman magani yayin da ake kwantar da mutum fiye 280 a duk mako sakamakon cutar a cibiyoyi biyu na masu fama da cutar da ke Kano.
Haka kuma Gidauniyar Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta bayyana cewa, Jihar Kano ne ke da kashi 80 na masu dauke da cutar Mashako a Nijeriya.
Wadanda cutar ta fi kamawa sun hada da mata da yara kanana masu shekaru kasa da biyar a duniya, sune cutar ta fi farmaka.
Da farko ya kamata kasashen duniya su hada kai da Nijeriya ta hanyar kawo mata gudummawa don yaki da cutar, ya kuma kamata a kawo karshen karancin maganin rigakafin, a kuma tabbatar da an samar da isassun magunguna a sassan Duniya.
A ra’ayinmu, wannan ba wai maganar kamar ana taimakon Nijeriya ba ne, al’amari ne da ya shafi lafiyar duniya gaba daya. Cutar ba Ruwan ta da iyaykokin kasa da kasa, in har ba a dauki matakin da ya kamata ba, za ta iya zama wata matsala da barazana da lafiyar duniya.
Bugu da kari kuma, dole ne Nijeriya ta kara kaimi wajen gudanar da rigakafi ga al’umma, a tattabatar da kowanne yaro ya samu allurar rigakafin cutar Mashako don shi ne hanya mafi sauki ta kariya daga cutar. Ya kamata a zafafa fadakar da al’umma don kawar da camfe-camfen da ake da shi a kan karbar rigakafi, wanda daga dukkan alamu yana kawo cikas ga shirin a wasu yankuna.
Domin tabbatar da kare yaduwar cutar a kwai bukatar daukar matakan ganowa tare da kebe wanda ke dauke da cutar don kare yaduwarsa daga wuri zuwa wuri. Akwai kuma bukatar a samar da issasun magunguna tare da horars da ma’aikatan lafiya a kan hanyoyin da za su fuskanci masu cutar da kare kansu a lokaci daya.
Muna kira ga gwamnatoci da al’ummar duniya da kuma dukkan masu ruwa da tsaki da su hada hannu don kawar da cutar Mashako a Nijeriya, martaninmu mu shi ne zai tabbatar da kariya ga dubban ‘yan Nijeriya a cikin gida dama kasashen waje.
Wannan kuma ya kamata ya zama wani abin da zai farkar da Nijeriya da sauran kasashen duniya na bukatar su karfafa cibiyoyin kiwon lafiyansu, karfafa tsarin rigakafinsu da kuma kara zuba jari wajen samar da asibitoci da cibiyoyin lafiya a yankunan karkara da kuma samar da su a kusa da al’umma don inganta lafiyar al’umma gaba daya.
Camfe-camfe a kan maganin rigakafi yana daga cikin manyan matsalolin da yaki da cutar Mashako ke fuskanta, a kan haka dole a kara kaimi wajen fadakar da al’umma tare da nuna musu cewa, wannan abu ne da ya shafi lafiyarsu dana ‘ya’yansu. Ya kuma kamata a hada da ta shugabannin al’umma kamar masu unguwanni, sarakuna da sauransu.
Abin da ya kamata mu fahimta a nan shi ne, yadda aka samu barkewar cutar mashako a Nijeriya yana nuna mana cewa, wasu cututtuka masu yaduwa da aka manta da su suna iya sake bullowa idan kuma yi sakaci. Dole al’umma duniya su hada hannun don kawo dauki tare da maganin cutar Mashako a kasar nan, wannan lokaci ne na daukar mataki ba sai anjima ba musamman ganin abu ne da ya shafi rayuwar al’ummar duniya baki daya.