Labaran yadda ake cin zafarafin yara gida masu aikatau a sassan Nijeriya na da tayar da hakula. Yara kan yi aiki ne ba dare ba raba yayin da masu gidansu ke musguna musu. Ana biyansu abin da bai taka kara ya karya ba a wasu wuraren ma ba a biyansu ko kwabo.
Ba wai yaki ne ya ci rayukan iyayen su ba, amma iyayen nasu ne suka mika su ga masu safarar su zuwa wajen aikatau din saboda tsanannin matsalar tattalin arzkin da suke ciki.
- Gwamna Uba Sani Ya Taya Kansa Murna Da Hukuncin Da Kotun Zaben Kaduna Ta Yanke
- Al’adun Kasar Sin Na Da Tushen Neman Zaman Lafiya Tun Lokacin Da
Dan abincin da aka rage suke samu su ci, shi ne kuma kadai abin da ke kwantar musu da hankali.
Binciken da jaridar LEADERSHIP Hausa ta yi, ya nuna cewa, daukar yara aikin aikatau yana matukar karuwa a ‘yan shekarun nan a sassan Nijeriya.
Labaran halin da yara masu aikatau ke ciki yana tayar da hakula, yana kara nuna irin muguntan da ake nuna wa yara ‘yan aiki a gidajen da suke zaman aikatau.
Labarin Bolutife, ‘yar shekara 13, ta uku ga wasu iyalai matalauta a garin Akure ta Jihar Ondo, lamarinta tamkar iyayenta sun mika ta zuwa rayuwar bauta ne da kansu. A ranar da abin ya faru, wata rana ce a watan Yuni na shekarar 2022, ta ga mahaifinta mai suna Olumide, dan shekara 54, yana tattauanwa da wasu baki daga Abuja a cikin falon gidansu. Daga baya ta fahinci cewa sune wadanda za su dauke ta aiki sune kuma za su ci gaba da cin zarafinta. Bolutife ta zama ‘yar aiki kuma baiwa haka kuma wanda ya dauke aiki ya zama da ita tamkar matarsa yana lalata da ita a kan dan abin da bai taka kara ya karya ba da yake ba iyayenta.
A halin yanzu tana nan ta fara farfadowa bayan da ta yi wata 8 ana musguna mata. Ta samu ‘yanci ne bayan da wata kungiya mai zaman kanta ta ceto ta.
Amma ba duka suke samun irin wannan sa’ar ba, misali, labarin Jemilah ya fara ne a ranar 7 ga watan Yuli na shekarar 2016 a garin Legas inda mutumin da ta ke yi wa aiki cikin fushi saboda bata wake buta yadda yake so ba ya ji mata ciwon da ya kai ga makancewarta a ido daya har a abada. Abin takaicin shi ne yarinyar ‘yar shekara 12 ta yi kokarinta na ganin ta ganmsar da uban dakin nata amma shi bai gani ba.
A wani lamari kuma da ya faru a garin Ikorodu ta Jihar Legas a ranar 19 ga watan Disamba 2016, wata mata mai yara uku wadda ya kamata ta zama mai kare rayuwa tare da shiryar da yara kamar yadda take yi wa yaranta amma sai ta zama sanadiyyar mutuwar ‘yar aikinta mai suna Faith, ‘yar shekara 10. Wannan lamarin ya tayar da hakulan al’umma kwarai da gaske.
Haka kuma a ranar 20 ga watan Mayu 2017. Wata ‘yar kasuwa ta yi wa ‘yar aikinta dukan kawo wuka inda dukan ya yi sanadiyyar mutuwarta, matar wadda ke daukje da ciki ta yi kokarin batar da gawar yarinyar amma asirinta ya tonu, daga nan doka ta yi halinta a kanta
Bincike ya kuma nuna yadda a watan Maris na shekarar 2018, aka samu irin wannan lamarin a birnin Legas, inda wata ‘yar aiki mai shgkara 10 a duniya ta kusan shekawa barzahu, laifinta kwai shi ne ta yi kokarin fada da yaran wadanda suka dauke ta aiki. Amma hukuncin da aka yi mata ya fi ainihin laifin da ta yi don kuwa an yi amfani da dutsen guga ne mai zafi ana dosanata mata a jiki, inda ya haifar da tabo masu yawa a jikinta.
An kuma samu irin wannan labarin a ranar 23 ga watan Afrilu na shekakar 2018, a Jihar Anambara, inda wata mai suna Uche Ugochukwu ta fito da maitarta da kuma tsananin muguntanta a kan ‘yar aikinta mai shekara 12, ta yi mata dukan kawo wuka abin da ya yi sanadiyyar ji mata ciwo a cikinta ya haifar mata da ciwon da za ta gama rayuwarta da su don ya shafi mahaifarta da wasu sassan hanjinta gaba daya.
Kididdiga daga Hukumar Kwadago ta Duniya (ILO), ya nuna cewa, yara fiye da Miliyan 15 ke aikin aikatau a Nijeriya. Aikatau na yara na nufin duk wani aiki da za a iya sa yara da zai hana su cin gajiyar yarintarsu, wanda kuma zai iya hana su halartar makaranta a lokacin da ya dace wanda kuma zai iya cutar da su ta kowacce hanya, kamar yadda kundin Wikipedia na shekarar 2022 ya zayyana.
Aikatau na yara abu ne da ya zama annoba a Nijeriya, yana kuma ci gaba da yaduwa. Amma in aka yi la’akari da halin da ake ciki a wannan zamanin, za a fahimci cewa, akwai yiwuwar a tura yara mata kashi 80 zuwa harkar aikatau fiye da yara maza. Yayin da dokar kare hakkin yara ya ayyana shekara 18 a matsayin shekarar da za a iya daukar yaro aiki amma kuma dokar kwadago ta sanya shekara 12 a mastayin shekarar da za a iya daukar yara aiki a saboda haka dole a daidaita dokar don a iya amfani da ita wajen hukunta masu ci da gumin yara kanana.
Karin bayani a rahoton UNICEF na shekarar 2021 ya nuna cewa yaran da ake aikawa aikatau masu shekara 5 zuwa 7 sun kai kashi 11. Wanda wannan ya karya dokar kare hakkin yara na shekarar 2003 da kuma doka kare yara da musguna musu na shekarar 2015.
A shekarar 2018 hukumar kare sarafar mutane (NAPTIP) ta bayyana cewa, dokarta ta shekarar 2015 ta samar da cewa, karya doka ne daukar yara masu shekara kasa da 12 duk wani nau’in aiki, za kuma a iya hukunta duk wanda aka samu da laifin yin haka.
Wani dan rajin kare hakkin al’umma mai suna Sunday Nwitie, ya ce hanyar samar da cikakken nasara a wannan fafutukar yana bukatar daukar mataki mai karfi.
Ya ce, ‘‘Ya kamata a fahimci muhimmanci yaranta ga yaranmu, a kuma hada hannu da al’umma ta yadda za a samar da wasu hanyoyin maye gurbin amfani da yara kanana a wajen ayyukan yau da kullumn na cikin gida. A kuma samar wa da yara sana’o’in dogaro da kai, irin wannan hanyar ne kuma aka bar mu a baya a kansu.
‘‘Dokar kare hakkin yara na shekarar 2003 na Nijeriya ya bayyana cewa, yaro ne shi ne wanda yake kasa da shekara 18, kuma dole a yi la’akari da abin da yake so a duk wani abin da za a yi da zai shafi rayuwarsa. Dokar ta yi tir da duk wani na’uin ci wa yaro mutunci da ya hada cin zarafinsa, dokar ta kuma haramta jefa yara cikin kangin bauta. Yayin da jihohi da dama a Nijeriya suka fara aiki da dokar, har zuwa wannan lokacin wasu basu iya fara aikata dokar ba saboda abubuwan da suka shafi al’ada da sauransu.’’
A cewar wani lauya mai zaman kansa mai suna, Richard Udoh, dogaro ga dokoki ba zai kai ga maganin cin zarafin yara a wajen aikatau ba, dole a hada da abin da suka shafi al’adun al’umma da addinansu. Shi ma wani lauya mai suna Felid Okoh, ya kalubanci yadda babu wani doka na musamman da aka shirya da zai kare yara daga cin zarafain da ake yi musu, ya ce, ba yadda dokoki za su yi aiki in har babu ilimi da kyakyawar kiwon lafiya ga al’umma.
Amma kuma wani ma’aikacin gwamnati mai suna, Deji Agbede, ya mika laifin ne ga abin da ya shafi al’adu, a akan haka ya ce, akwai bukatar a sa shugabannin al’umma a yakin da ake yi da wannan lamarin. In har aka ci gaba da bautar da yara hakan na faruwa ne saboda al’umma na amfana daga abin da ke fitowa ne daga lamarin.
A ta bakin wani lauya mai suna James Udeh, ya ce amfani da yara kanana a matsayin ‘yan aiki a gidaje abu ne mai tayar da hankali, ya kuma ce ya kamata a yi yaki da wanna halin ta dukkan hanyar da ya dace, Ya kara da cewa, lamarin yana karuwa ne a wuraren da aka fi dandana tsananin matsalar tattalin arzikin a cikin yankunan Nijeriya.
Ya ce, ‘‘Ana daukar yara kanana da shari’a ba ta amince da yin haka don su yi wasu ayyuka a gidaje da suka hada da wanke-wanke ana kuma basu wasu kdade da basu taka kara sun karya ba. Yawancin ‘yan aikin da muke da su a Nijeriya kananan yara ne da doka bata amince da shekarun su ba, suna kuma fitowa ne daga iyalai matalauta ana aikasu zuwa gidajen masu kudi don yin aiki. Babu wahalar da ‘yan aikin basa fuskanta, tun daga musgunawa har zuwa rasa rayuwuka, da yawansu ba a tura su makaranta, wanda kuma yakan kasance cikin sharadin da akan yi na bayar da su aikin tun da farko. Ana dorawa wadannan ‘yan aikin manyan ayyukan da ya fi karfinsu tare da kuma bata lokacin wajen kula da yaran wadanda suka dauke su aiki, sune na farkon tashi kuma na karshen barci. Ba a basu abinci isasshe suna kuma kwanciya ne a kicin ko kuma wani wuri mara kyau.
Wani abin lura anan kuma shi ne yadda ake amfani da wasu ‘yan kwamisho wajen nemo tare da daukar ‘yan aikin. Suna amfani da hanyoyi daban-daban wajen cimman manufar su wanda suka hada da ziyartar kauyyuka suna yi wa iyayen yara dadin baki na za su samar wa yarasu aiki a birane. Ana kwaso ‘yan matan daga kauyukansu zuwa birane kamar Legas, Abuja, Fatakwal da wasu garuruwa da zaran iyayensu sun amince. Yaran sun zama kamar wata hanyar samun tallafi na tattalin arziki ga iyayensu wadanda ke cikin matsanancin bukata. Saboda haka wai a ce ana kula da yaransu yana kuma ana turo musu kudade wani abu ne da mutane da dama za su yi maraba da shi, akan bayar da yaran ne ba tare da wani ciakken binciken sanin halin wanda za a ba yaran ba, don sanin ko mutanen kirki ne ko a a.
Sai dai kuma bincikenmu ya nuna cewa, da yawa daga cikin wadanda suke daukar yaran suna bukatar sai an yi wa yaran gwaje-gwaje don gano ko suna dauke da cututtuka kamar cutar Kanjamar, cutar hanta da cutar tarin fuka, in aka gudanar da gwaje-gwajen aka gano wani ko wata daga cikin yaran na dauke da wani cuta a kan ki daukarsa sai a koma da shi gida don kada ya harbi mutane da zai yi wa aiki.
Wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Simbi Foundation’, ta bayyana cewa, daga cikin dalilan da ya sa ake tura yara aikatau sun hada da rashin ilimi, talauci da kuma wasu al’adun al’umma da wasu suka runguma.
Jaridar LEADERSHIP ta kuma gano cewa, cikin matsalolin da bautar da yara yake haifarwa sun hada da nakasa ilimi, cin zarafin yara da kuma nakasa girmansu da hana su cimma burinsu na rayuwa.