Uwar gidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma jakadiyar UNESCO ta musamman mai kula da inganta aikin ba da ilmi ga yara mata da mata Peng Liyuan da babbar darektar UNESCO Audrey Azoulay, sun halarci bikin ba da lambar yabo ga ayyukan ba da ilmi ga yara mata da mata na UNESCO na shekarar 2023 da aka yi jiya da safe a nan birnin Beijing.
Da take gabatar da jawabi, Peng Liyuan ta bayyana cewa, a duniyar yau, aikin ba da ilimi ga mata manya da kanana na fuskantar sabbin yanayi, da sabbin bukatu, da kuma sabbin kalubale. Tana fatan mutane masu yawa za su sadaukar da kansu ga aikin, tare da taimakawa mata masu yawa su canza makomarsu da fahimtar darajar rayuwarsu ta hanyar samun ilimi.
- Yadda Alakar Sin Da Afirka Ke Kara Bunkasa Kasashen Nahiyar Afirka
- Tunanin Gina Al’ummar Duniya Mai Makomar Bai Daya Ya Haskaka Makomar Duniya
A nata bangaren, madam Azoulay a cikin nata jawabin, ta godewa gwamnatin kasar Sin bisa goyon baya mai karfi da take bayarwa ga UNESCO, da kuma Farfesa Peng Liyuan, bisa irin gudummawar da ta bayar wajen inganta aikin ba da ilmi ga yara mata da mata a duniya. Ta kara da cewa, hukumarta na fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwa da kasar Sin don sa kaimi ga ci gaban harkar ba da ilimi ga yara mata da mata a fadin duniya.
Lambar yabo ta ayyukan bayar da ilimi ga mata da ‘yan mata, ita ce irinta daya tilo da UNESCO ke bayarwa ga shirye shiryen ba da ilimi ga yara mata da mata. Kuma a bana, shirin “Spring Bud Project” na kasar Sin da shirin “Star School Program” na Pakistan sun samu wannan lambar yabo. (Mai fassara: Bilkisu Xin)