Yau rana ce ta bikin tsakiyar yanayin kaka na gargajiya na kasar Sin. Bikin wannan rana na dauke da kyawawan fatan jama’a na neman haduwa da juna, kuma yana kunshe da kaunar da jama’a ke nunawa gida da kasarsu.
A jajibirin bikin tsakiyar yanayin kaka na shekarar 1986, Xi Jinping, wanda ya kasance mataimakin magajin birnin Xiamen a lokacin, ya hau keke, ya kai kwalayen wainar wata zuwa dakin kwanan daliban jami’ar Xiamen, don murnar bikin tare da su, wanda hakan ya sanya daliban da suka bar gidajensu jin tamkar suna gida.
- CMG Ta Kaddamar Da Bikin Fara Nuna Shirin “Journey Through Civilizations” A Hong Kong Da Macau
- Yadda Bankuna Suka Ci Bashin Naira Tiriliyan 3.03 Daga CBN A Cikin Kwana 22
A cikin shekarun da suka gabata, saboda yadda a ko da yaushe Xi Jinping ya ke damuwa da matasan dake karatu a wasu wurare ko kuma masu yawo da ke nesa da garuruwansu, a duk wani muhimmin bikin gargajiya, ya kan aike da fatan alheri ga kowa da kowa.
A jajibirin bikin tsakiyar kaka na shekarar 2015, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci liyafar maraba da zuwa da jama’ar Sinawa mazauna kasar Amurka a birnin Seattle suka shirya masa, inda ya bayyana fatan alheri ga Sinawa mazauna kasar, ya kuma ce “Mun zo Amurka a wannan karo ne don kawo muku wainar wata daga kasarmu, wannan karamar kyauta ce daga jama’ar kasarmu.” (Mai fassara: Bilkisu Xin)