• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Danbarwar Auren Sadiya Haruna Da G-Fresh Ta Dawo

by Abba Ibrahim Wada
2 years ago
Auren

Kotun  sharia’r musulunci dake zamanta a filin hoki dake Kano ta  umarci mai barkwancin nan na manhajar TikTok, Abubakar Ibrahim da aka fi sani da  G-Fresh da ya koma yayi bikon matarsa, sayyada Sadiya Haruna, wadda aka ruwaito cewa tayi yaji.

Kamar yadda kotun ta bayyana, tunda G Fresh bai saki matarsa ba akwai bukatar yayi bikon ta domin ci gaba da zaman aure kamar yadda addinin musulunci ya tsara ga duk wadda tayi yaji.

  • Kotu Ta Kori Kakakin Majalisar Dokokin Filato
  • Yadda Alakar Sin Da Afirka Ke Kara Bunkasa Kasashen Nahiyar Afirka

Lauya mai kare G Fresh Barr. Fatima Aliyu ta bayyana cewar har yanzu G Fresh na matukar kaunar matar sa wanda hakan yasa ba zai iya rabuwa da ita ba kuma shima G-Fresh din yasha nanatawa a shafinsa na TikTok cewa yana son matarsa kuma ba zai iya rabuwa da ita ba.

Kotun dai ta bayar da daga yau zuwa ranar 10 ga watan Oktoba mai kamawa domin G Fresh ya sulhunta da matarsa Sayyada Sadiya Haruna kuma ta koma su ci gaba da zaman auren su.

A kwanakin baya ne dai aka dinga yada wata jita-jita cewar auren taurarin Tiktok din, Sayyada Sadiya Haruna da G-Fresh Al-Ameen  Kano state material ya mutu, sai dai daga baya ya fito ya bayyana cewa auren yana nan daram ba kamar yadda ake ta yayatawa ba.

LABARAI MASU NASABA

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

A ranar 16 ga Yunin da ya wuce ne aka daura auren shahararrun masoyan na TikTok, auren da ya dauki hankulan mutane da dama musamman masu amfani da kafofin sada zumunta na zamani da suka hada da Facebook da D da kuma TikTok din.

Sai dai Jim kadan bayan tarewar Ango a gidan Amarya kuma sai ta tafi aikin Hajji a kasa mai tsarki wanda hakan tasa G-Fresh kullum ya dinga yada bidiyon sa, yana sambatun shaukin rabuwa da amaryarsa.

Amma bayan dawowar amarya sai ga labari ya cika TikTok da sauran kafafen sada zumunta cewa wai auren taurarin biyu ya mutu inda har ma wasu ‘yan TikTok na cewa wai G-fresh ya yi yaji ne daga gidan Sayyada Sadiya ya koma kwanan shago bayan da aka samu sabani a tsakaninsu.

Amma daga baya kuma aka gano cewa har yanzu Al-ameen G-fresh Kano state material ya na nan a dakin matarsa Sayyada Sadiya Haruna kuma shima ya nanata hakan.

Wasu rahotanni sun ruwaito cewar tun farko Sayyada Sadiya ta mayar da shafinta na TikTok wurin tallata magunagunan gargajiya da take sayarwa kuma ta goge duk wani bidiyo da ta yi a baya ciki kuwa har da bidiyoyin soyayyarsu da Kano state material din.

Sai dai goge bidiyon ne yasa wasu  suka fara yada jita-jitar cewa an samu matsala tsakanin ma’auratan guda biyu wadanda soyayyar su ya karade ko ina a shafukan sada zumunta.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
Nishadi

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 
Nishadi

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

October 11, 2025
Next Post
Za A Wallafa Sharhin Xi Kan Ciyar Da Zamanantar Da Kasar Sin Gaba

Za A Wallafa Sharhin Xi Kan Ciyar Da Zamanantar Da Kasar Sin Gaba

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara

November 4, 2025
‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

November 4, 2025
tinubu

Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU

November 4, 2025
Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

November 4, 2025
2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC

2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC

November 4, 2025
Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

November 4, 2025
Karancin Abinci: Kofar Ofishin Tinubu A Rufe Take, Har Wasu Ministoci Ba Su Iya Ganinsa – Ndume 

Zargin Kisan Kiyashi Ga Kiristoci: Trump Bai San Ƙalubalen Tsaron Da Najeriya Ke Ciki Ba — Ndume

November 4, 2025
Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

November 4, 2025
Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

November 4, 2025
Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.