A safiyar ranar Litinin ne aka gurfanar da tsohuwar ministar albarkatun man fetur ta Nijeriya, Diezani Alison-Madueke, a gaban wata kotun majistare ta Westminster da ke birnin Landan da laifin karbar cin hanci bayan wani bincike da hukumar yaki da laifuka ta kasar Birtaniya NCA ta gudanar.
Diezani Alison-Madueke, mai shekaru 63, wadda kuma ta zama shugabar kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC, ta kasance jigo a gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015.
- Tinubu Ya Amince Da Biyan Ma’aikata Karin Albashin N35,000 Na Wucin Gadi
- Ranar ‘Yanci: Tinubu Ya Kara Wa Kananan Ma’aikata N25,000 Kan Albashinsu
A cewar NCA, Diezani ta karbi cin hanci a lokacin da take rike da mukamin ministar albarkatun man fetur a maimakon ta ba da kwangilolin man fetur da iskar gas na fam miliyan.
Ana zarginta da cin tsabar kuɗi har £100,000, motoci da jirage masu saukar ungulu masu zaman kansu da tara kayan alatu ga iyalint da kuma tara kadarori a London da daman gaske.
Har ila yau tuhume-tuhumen nata sun yi cikakken bayanin game da kayan da ake zarginta sama da fadi da su.
Aliso-Madueke, wacce a halin yanzu ke zaune a St John’s Wood, London, ta bayyana a Kotun Majistare ta Westminster a ranar Litinin, 2 ga Oktoba, 2023.
A ranar 22 ga watan Agusta ne LEADERSHIP ta gabatar da rahoton shugaban sashin yaki da cin hanci da rashawa na NCA (ICU), Andy Kelly, yana mai cewa: “Muna zargin Diezani Alison-Madueke ta yi amfani da karfinta a Nijeriya kuma ta karbi tukuicin kudi ta bayar da kwangiloli na miliyoyin ta hanyar da bata dace ba.