Kotu a birnin New York ta fara sauraron tuhumar da masu gabatar da kara ke yi wa tsohon shugaban Amurka Donald Trump, kan aikata laifin zamba a harkokin kasuwancinsa.
Shari’ar dai ta kara dagula wa Trump lissafi dangane da yunkurinsa na neman sake darewa kujerar shugabancin Amurka, gami da kara yawan tuhume-tuhumen da yake fuskanta a kotuna.
A lokacin da ya bayyana gaban kotun ta New York, Trump ya yi amfani da kakkausan harshe wajen caccakar masu kararsa da kuma alkalin da ke sauraron shari’ar, wadda ya bayyana a matsayin bita da kulli mafi muni da aka shirya tarihin kasar Amurka.
Babbar mai gabatar da kara Letitia James na neman kotu ta tilasta wa Trump biyan tarar akalla dala miliyan 250, da kuma haramcin kasuwanci na dindindin a birnin New York ga tsohon shugaban da iyalansa.
Shari’ar da Trump ke fuskanta dai ta mayar da hankali ne kan zarginsa da kara kimar kamfanin kasuwancinsa na Trump Organisation da gangan don azurta kansa.
Mai gabatar da karar ta ce binciken da ta gudanar ya bankado yadda tsohon shugaban Amurkan ya wallafa rahoton da ke nuna cewar arzikinsa ya kai dala biliyan 6 da miliyan 100, bayan kuma yana sane cewar dala biliyan 2 da miliyan 600 ya mallaka.
Muddin kotu ta samu tsohon shugaban da laifi, zai iya biyan tara mai nauyi da kuma yiwuwar rasa lasisin kasuwancinsa.