Kimanin ‘yan kasuwa 40 ne suka rasu a hatsarin jirgin ruwa a kogin Neja a yayain da suke akan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Yauri da ke a jihar Kebbi.Â
An ruwaito cewa, jirgin wanda ke dauke da ‘yan kasuwa su 50 tare da hajarsu ya taso ne daga kauyen Kasabo zuwa garin Yauri a ranar Litinin don zuwa cin kasuwa, inda bayan Igiyar ruwa ta kada, ya kife.
- MDD Da NSCC Sun Yi Bikin Ranar Tsofaffi Ta Duniya Ta 2023
- Juyin Mulki: An Sake Bude Makarantu A Nijar Bayan Wata 3
Sai dai, an ruwaito cewa, masu ceto, sun samu nasarar ceto mutum 10 inda kuma har yanzu, ba a iya gano fasinjiji 40 ba.
Bugu da kari, an ruwato cewa, a ranar Talata an samu nasarar gano gawarwakin fasinjoji shida.
Rahotanni sun sanar da cewa, a watan Satumbar da ya wuce, kimanin mutane guda 936 suka rasu a hatsarin jirgin ruwa daban-,daban a sassan kasar nan.
Shugaban karamar hukumar Yauri, Alhaji Bala Mohammed wanda ya tabbatar da adadin fasinjojin da suka rasu, ya sanar da cewa, har yanzu masu ceto na kan ci gaba da neman sauran fasinjojin da suka bace a cikin kogin.
Kazalika a ta’aziyyarsa a lokacin da ya kai ziyara a garin na Yauri a ranar Litinin, gwamnan jihar Nasiru Idris, ya yi addu’ar fatan samun lafiya ga fasinjojin da suka samu raunuka tare da yin fatan kare sake aukuwar hatsarin a nan gaba.