ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Juyin Mulki: An Sake Bude Makarantu A Nijar Bayan Wata 3

by Sadiq
3 years ago
Nijar

Bayan dogon hutu na watanni uku, an sake bude makarantun boko a Jamhuriyar Nijar, yayin da kasar ke ci gaba da fadi-tashin yadda za ta tunkari kasashen kungiyar ECOWAS da ke barazanar tura mata dakarun soji.

To sai dai komawa makarantar a wannan karo, ya zo ne a cikin wani yanayi, sanadiyyar takunkuman da aka kakaba wa kasar bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin dimokuradiyya.

  • Jama’a A Fadin Kasar Sin Na Bikin Ranar Kafuwar Kasar Yayin Da Suka Shiga Lokacin Hutu Mai Tsawo
  • Tawagar Masu Aikin Na’urar Binciken Duniyar Wata Mai Suna Chang’e 5 Ta Kasar Sin Ta Samu Babbar Lambar Yabo

A ranar 26 ga watan Yuli aka wayi gari da labarin cewar sojojin da suke tsaron fadar shugaban kasa, a karkashin jagorancin Janar Abderahmane Tchiane sun tsare shugaba Bazoum a cikin fadarsa, abin da ya jefa fargaba a ciki da wajen kasar.

ADVERTISEMENT

Daga bisani, sojojin sun yi sanarwar kawar da shugaba Bazoum da kuma tsare shi tare da wasu ministocinsa saboda wasu dalilai da suka bayar wanda ya shafi tsaron kasa da kuma irin barazanar da Nijar ta ke fuskanta.

Kazalika sojojin sun sha suka daga kasashe da dama kan tsare shugaba Bazoum ciki har da mukarrabansa.

LABARAI MASU NASABA

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

Saudiyya Ta Ɗage Babban Taron Zuba Jari Zuwa Shekarar 2027

Kazalika, ECOWAS ta yi yunkurin daukar matakin soji a kan sojojin da suka kifar da gwamnatin dimokuraddiya a kasar.

Sai dai al’amura na ci gaba da daidaita yayin da gwamnatin sojin kasar ke neman sake kulla alaka da wasu kasashe.

MASU ALAKA

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh
Kasashen Ketare

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Saudiyya Ta Ɗage Babban Taron Zuba Jari Zuwa Shekarar 2027
Kasashen Ketare

Saudiyya Ta Ɗage Babban Taron Zuba Jari Zuwa Shekarar 2027

October 20, 2026
An Kashe Mutane 18 A Harin Houthi Kan Sansanin Sojoji A Yemen
Kasashen Ketare

An Kashe Mutane 18 A Harin Houthi Kan Sansanin Sojoji A Yemen

October 19, 2026
Next Post
Sharhi: Shin Tinubu Zai Iya Kai Bantensa Bisa Yadda Ya Fara?

Jami'ar Chicago Ta Tabbatar Da Sahihancin Shaidar Karatun Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Uku Da Aka Sace A Kebbi

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Uku Da Aka Sace A Kebbi

October 25, 2026
Ana Buƙatar Ɗaukar Matakai Masu Tsauri Domin Ci Gaban Nijeriya – Wike

Ana Buƙatar Ɗaukar Matakai Masu Tsauri Domin Ci Gaban Nijeriya – Wike

October 25, 2026
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Tura Dakarunta Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Yankin Olle-Bunu Na Jihar Kogi

Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 15 Ta Harin Sama A Borno

October 25, 2026
2027: Hana Tinubu Wa’adi Na Biyu Na Iya Jefa Nijeriya Cikin Rikicin Siyasa — Pakistan

Tinubu Ya Cancanci A Sake Zaɓensa A 2027 — Pakistan

October 25, 2026
Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Harin Jihar Taraba Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 40

Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Harin Jihar Taraba Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 40

October 25, 2026
Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo

ADC Ta Yi Wa APC Ba’a Kan Zargin Hayar Taron Jama’a Da Rashin Cika Kujeru A Taron Kaduna

October 25, 2026
An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026
EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.