Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce kasar na maraba da ziyarar shugaban masu rinjaye na majalisar dattijan Amurka, Chuck Schumer.
Ma’aikatar ta bayyana haka ne yau Laraba, bayan Schumer ya sanar da cewa zai jagoranci wata tawagar sanatoci daga jam’iyyu biyu na kasar zuwa kasar Sin a ‘yan kwanki masu zuwa.
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar na cewa, kasar Sin na fatan ziyarar za ta bayar da gudunmuwa wajen kara fahimtar kasar Sin a majalisar dattijan Amurka da kara tattaunawa da tuntuba tsakanin majalisun dokokin kasashen biyu, har ma da inganta habakar dangantaka tsakanin Sin da Amurka. (Fa’iza Mustapha)