Hukumar shige da fice ta Nijeriya (NIS) ta samar da fasfo 204,332 cikin makonni uku.
Da ta ke yiwa manema labarai jawabi a Abuja, Mukaddashiyar Kwanturola Janar ta NIS, Mrs Caroline Wuraola-Adepoju ta ce, kalubalen da hukumar ke fuskanta a yanzu shi ne, mutane 91,981 ne kacal cikin adadin suka karbi fasfo din su.
- Tirka-tirkan Takardun Tinubu: Ku Zo Mu Hada Hannu Don Fafutukar Wanzar Da Gaskiya – Atiku Ya Roki Obi, Kwankwaso
- Saura ‘Yan Watanni Ya Sauka A Mulki, Gwamna Bello Ya Nada Mataimaka 215
Ta bayyana cewa, an samu wannan nasarar ne sakamakon kafa dokar ta-baci kan samar da fasfo akan lokaci yayin da ta amshi ragamar shugabancin hukumar a watannin da suka gabata.
A cewarta, zuwan sabon ministan harkokin cikin gida, wani karin guiwa ne hukumar ta samu wurin zage damtse domin ganin an shawo kan kalubalen samar da fasfo akan lokaci.
Don haka, shugabar ta yi kira ga ’yan Nijeriya da suka bukaci fasfo din da su zo su amshi abinsu ba tare da sake biyan ko taro ba.
Wasu daga cikin matakin da hukumar ta dauka da suka kai ga samun wannan nasara, a cewar Adepoju su ne, an kara yawan jami’ai a cibiyar samar da fasfon sannan kuma abokan huldar hukumar sun kara yawan injinan buga fasfon.
Ta kuma bukaci ‘yan Nijeriya da ke da korafi da su kira Sashen SERVICOM ta lamba 08067761996 da jami’in hulda da jama’a na hukumar NIS a lamba 08038125789.