Manchester United zata karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Brentford a babban filin wasa na Old Trafford dake birnin Manchester.
Wannan shine wasan sati na 8 na gasar Firimiyar kasar Ingila da ake cigaba da fafatawa.
- Abin Da Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Leipzig Da Manchester City
- Hasashe Yadda Wasan Manchester United Da Burnley Zai Kaya
Manchester United ta hadu da Brentford sau 16 a tarihi,inda Manchester United ta samu nasara sau 7 akayi canjaras 3 sai kuma Brentford da ta samu nasara sau 6.
Manchester United da ke matsayi na 10 akan teburin Firimiya na fatan ganin ta samu nasara akan Brentford dake matsayi na 14.