Masana’antar sarrafa karfe ta Smederevo da aka kafa a shekarar 1913, ta taba kasancewa abun alfahari a kasar Serbia, duba da yadda ta taba samar da kudin shiga har kaso 40 bisa dari na gwamnatin birnin Smederevo. Amma, masana’antar ta kusan durkushewa, sakamakon tsananin gasar kasuwanni.
A watan Afrilu na shekarar 2016, bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”, kamfanin sarrafa karfe na HBIS na kasar Sin, ya zuba jarin kudi har Euro miliyan 46, domin kafa reshen kamfanin sarrafa karfe na HBIS a kasar Serbia.
- Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Kama Hanyar Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba A Yankin Tsaunin Himalaya
- Kazakhstan, Kasa Marar Ruwa Mafi Girma A Duniya, Tana Da Nata Hanyar Shiga Teku
Kuma, bayan watanni biyu da kafa kamfanin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara wurin, inda ya bayyana cewa, hadin gwiwar kamfanoni tsakanin kasar Sin da kasar Serbia, ya bude sabon babin hadin gwiwar bangarorin biyu a fannin makamashi. Kuma ya yi imanin cewa, bisa hadin gwiwarsu, tabbas, masana’antar sarrafa karfe ta Smederevo za ta farfado baki daya.
Kaza lika, bayan watanni 8 da kafa kamfanin, ya zuwa karshen shekarar 2016, masana’antar ta fara samun riba. Kuma, wannan kamfani ya fara shiga kasuwannin kasashen duniya, sakamakon sabbin fasahohin sarrafa karfe, da manufofin gudanar da harkokin kamfanin da kasar Sin ta shigar.
A halin yanzu, kimanin mutane dubu 20 suna gudanar da ayyukan dake shafar masana’antar sarrafa karfe a birnin Smederevo. Kana, adadin mutanen da suka rasa ayyukan yi ya ragu, daga kaso 18% zuwa 6%, kuma, adadin kudaden shiga da gwamnatin birnin ya samu ya ninka har sau biyu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)