An gabatar da tunanin Xi Jinping kan al’adu a yayin taron kasa na yini biyu game da ayyukan sadarwar jama’a da al’adu, wanda aka gudanar jiya Asabar zuwa yau Lahadi a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
A cewar taron, tun bayan babban taron JKS karo na 18 zuwa yanzu, an cimma nasarori masu dimbin tarihi a fannonin sadarwar jama’a da al’adu, inda aka danganta nasarorin da aka cimma ga jagorancin shugaba Xi Jinping, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS kuma shugaban rundunar sojojin kasar. An kuma gabatar da wani umarni da Xi ya bayar a baya-bayan nan a wurin taron.
A cikin wannan umarni, Xi ya jaddada da a karfafa kwarin gwiwa a fannin al’adu, da bin tsarin bude kofa da damawa da kowa, da kiyaye muhimman ka’idoji, yayin da ake neman cimma sabbin nasarori, don samar da tabbacin akida mai karfi, da karfi na ruhi, da yanayin al’adu masu kyau na gina kasa ta zamani mai salon gurguzu daga dukkan bangarori, da ciyar da babban burin farfadowar al’ummar kasar Sin a dukkan bangarori. (Ibrahim)