A gabannin bude taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa dangane da shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na 3, an gudanar da bikin kaddamar da sabuwar hadin gwiwa tsakanin babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG da kafofin yada labaru na kasashen da ke aiwatar da shawarar yau Litinin a nan Beijing, hedkwatar mulkin kasar Sin.
A yayin bikin, Shen Haixiong, shugaban CMG ya bayyana cikin jawabinsa cewa, a bana ake cika shekaru 10 da shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” da kuma tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam. CMG yana sauke nauyin dake bisa wuyansa, da shiga aikin aiwatar da shawarar, da ganewa idonsa yadda ake aiwatar da shawarar, da kuma watsa shirye-shirye kan yadda ake aiwatar da shawarar. Ya zuwa yanzu ya sa hannu kan yarjejeniyoyin watsa labaru da kafofin yada labaru 682 daga kasashe 151, ya kuma yi kira da a kafa kawancen kafofin yada labaru na duniya na farko bisa ga hanyar siliki, tare da rika inganta hadin gwiwar da ke tsakanin kafofin yada labaru na kasashen da ke aiwatar da shawarar.
Salihu Dembos, shugaban gidan talibijin na Najeriya na NTA ya bayyana cikin jawabinsa ta kafar bidiyo cewa, yana fatan ta hanyar kallon shirye-shiryen da za nuna a wannan karo, za a kara fahimtar sakamakon ci gaba da aka samu cikin wadannan shekaru 10, da yadda kasar Sin take gada da raya al’adun gargajiya, da kuma yadda Sin da kasashen da ke aiwatar da shawarar suke koyi da juna ta fuskar wayewar kai. (Tasallah Yuan)