Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin wasu mutum hudu da za su yi aiki a karkashin tawagar yada labarai da hulda da jama’a a ofishin shugaban kasa da za su kare martaba da kimar gwamnatin tarayya.Â
A wata sanarwa mai dauke da sanya hannun kakakin shugaban kasa, Ajuri Ngelale, a ranar Litinin na cewa, wadanda aka nada din su ne; Fela Durotoye, babban mataimakin shugaban kasa na musamman kan darajantawa da tabbatar da adalci ga jama’a; Fredrick Nwabufo, babban mataimakin shugaban kasa na musamman a bangaren wayar da kan jama’a; Linda Nwabuwa Akhigbe. babbar mataimakiyar shugaban kasa na musamman kan tsare-tsaren sadarwa.
- Babu Maganar Dawo Da Tallafin Man Fetur – NNPCL
- Rikicin Falasdinu Da Isra’ila: Saudiyya Ta Dakatar Da Duk Wata Tattaunawa Da Isra’ila
Sauran su ne Aliyu Audu, mataimaki na musamman kan harkokin jama’a da kuma mataimaki na kashin kai ga shugaban kasa (PA) a bangaren ayyuka na musamman da aka nada — Francis Adah Abah.
Ngelale ya kara da cewa shugaban Tinubu ya kuma sake amincewa da sakin mara ga Linda Nwabuwa Akhigbe domin ta yi aiki a matsayin mai bada shawara kan sadarwa ga shugaban hukumar ECOWAS.
Sanarwar ta ce, shugaban ya yi kira ga wadanda aka nadan da su yi aiki tukuru tare da amfani da gogewarsu da iliminsu wajen kyautata cigaban tattalin arzikin kasar nan.