Yau Talata 10 ga wata, ofishin watsa labarai na majalissar gudanarwar kasar Sin ya kira taron manema labarai, inda ya fitar da takarda mai taken “Shawarar ziri daya da hanya daya: Muhimmin jigo ga samar da al’ummar duniya mai makomar bai daya”.
A cikin takardar, an yi bayani kan tarihi, da buri, da dabaru, da sakamako, da ma’anar shawarar ziri daya da hanya daya, karkashin jagorancin tunanin Xi Jinping na tsarin gurguzu mai salon kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki, kuma an yi cikakken bayani kan babban sakamakon da aka samu a cikin shekaru goma da suka gabata, wato tun bayan da aka gabatar da shawarar, tare kuma da yin karin haske kan niyyar kasar Sin, da matakan da ta dauka yayin kokarin da take yi domin samun ci gaba mai inganci, bisa shawarar ziri daya da hanya daya, da kuma gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya tare da sauran kasashen duniya.
Takardar tana kunshe da sassa biyar, da suka hada da kasancewar shawarar mai asali daga kasar Sin amma ta rungumi dukkanin duniya, da neman hanyar samun wadata tare, da ingiza cudanya a fannoni daban daban, da sa kaimi ga zaman lafiya da ci gaban duniya, da habaka ci gaba mai inganci bisa shawarar ziri daya da hanya daya.
An wallafa takardar bayanan ne da harsuna takwas, wadanda suka hada da Sinanci, da Turanci, da Faransanci, da Rashanci, da Jamusanci, da harshen Spaniya, da Larabci da kuma Japananci. (Mai fassara: Jamila)