Wani rahoto da Jaridar Financial Times da ke Landan ta fitar, ya nuna cewa sauya fasalin tattalin arzikin Nijeriya da shugaba Bola Tinubu ya yi, alamu sun nuna cewa ba ya tafiyar da kasar kamar yadda aka tsara tun farko.
Jaridar ta ce, duk da cewa Tinubu ya fara da cire tallafin man fetur, abubuwan da suka faru a cikin watanni hudu da suka gabata sun nuna cewa dole ne gwamnatinsa ta tashi tsaye wajen ceto Nijeriya.
Financial Times ta shawarci shugaba Tinubu da ya daina bayyana tsare-tsaren tattalin arziki ba tare da tunanin yadda za a aiwatar da su ba.
A cewar jaridar, cikin watanni hudu da fara shugabancin kasar, akwai alamun tabarbarewar al’amura da dama daga gwamnatinsa.
Rahoton ya yi nuni da cewa, cire Godwin Emefiele, tsohon gwamnan CBN ya tayar da kura, domin kuwa maimakon a samar da ci gaba, sai al’amura suka kara tabarbarewa.
Dangane da yadda sabbin shugabannin CBN za su daidaita tsarin hada-hadar kudi kuwa, rahoton ya ce sabon shugaban bankin, zai iya kara yawan kudin ruwa domin dakile hauhawar farashin kayayyakin da ke addabar ‘yan kasar a halin yanzu.
Tuni dai wasu tsare-tsare da shugaba Tinubu ya kaddamar suka jefa kasar cikin matsin rayuwa, inda kayan masarufi ke ci gaba da yin tashin gwauron zabi.