Kungiyar magoya bayan Jam’iyyar APC – APC Cancanta, da ke jihar Kaduna, ta yi Allah wadai kan yadda aka wallafa hoton gwamnan jihar, Sanata Uba Sani na cece-ku-ce kan rabon mukaman siyasa da gwamnatinsa ta yi a kwanan baya.
Shugaban kungiyar, Habib Bello Chikaji ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
- Gwamna Uba Sani Ya Taya Sarkin Zazzau Murnar Cika Shekara Uku A Kan Karagar Mulki
- Zulum Ya Daukaka Darajar Kwalejin Larabci Zuwa Babbar Cibiyar Yaki Da Akidun Boko Haram
Habib, ya yi martani ne kan yadda kafar yada labarai ta BBC Hausa ta yi amfani da hoton Gwamna Uba Sani yana cece-ku-ce kan rabon mukaman siyasa da gwamnatin jihar ta yi a baya.
A makon da ya gabata ne, BBC Hausa ta wallafa wani rahoto da wasu ‘ya’yan Jam’iyyar APC a Jihar suka yi, inda suke kalubalantar Gwamnatin Uba Sani da cewa, ta mayar da su Saniyar ware wajen rabon mukamai a jihar.
Ya ce, kamata ya yi, BBC Hausa ta yi amfani da hoton ‘ya’yan Jam’iyyar APCn da ke korafin ba hoton gwamnan ba.
Habib, ya yi nuni da cewa, amfani da hoton gwamna Uba Sani a irin wannan rahoton, tamkar cin zarafinsa ne.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp