Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a biranen Jingdezhen, da Shangrao na lardin Jiangxi dake gabashin kasar Sin.
Xi Jinping, wanda ya ziyarci biranen a jiya Laraba, ya ganewa idanun sa wani rukunin gine ginen al’adun gargajiya masu tsohon tarihi, da kamfanin AVIC Changhe na kera jiragen sama dake birnin Jingdezhen. Kaza lika ya ziyarci wani kauye dake karkashin gundumar Wuyuan na birnin Shangrao.
Yayin wannan ziyara, ya kuma nazarci matakan da ake aiwatarwa na kariya, da gadon al’adun sarrafa kayan fadi-ka-mutu, da fasahohin kere-kere, da aikin kare muhallin halittun fadamu, da kuma raya kauyuka. (Saminu Alhassan)