A Ruwanda, mutum daya cikin duk mutane 30 na al’ummun kasar manomin kofi ne, amma cinikayyar kasa da kasa ba ta gudana yadda ya kamata a kasar, don haka manoman kofin Ruwanda ba su iya samun isasshen kudin shiga, kuma hakan ke sanya su fitar da danyen waken kofi zuwa ketare.
A watan Yulin shekarar 2018, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara kasar, inda a lokacin kasashen biyu wato Sin da Ruwanda, suka daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama, bisa tsarin shawarar ziri daya da hanya daya, ciki har da yarjejeniya mai nasaba da kasuwancin yanar gizo. Daga baya, an fara sayar da kofi mai tambarin Gorilla a kasar Sin ta yanar gizo. A sanadin haka, manoman kasar sun rika samun karin kudin shiga har dalar Amurka hudu idan sun sayar da kofi kilo daya.
Kasar Sin tana kokarin taimakawa Ruwanda wajen raya tattalin arziki na yanar gizo, lamarin da ya sa kaimi ga farfado da ci gaban tattalin arzikin kasar. An lura cewa, adadin karuwar GDPn Ruwanda a shekarar 2022 ya kai kaso 8.2 bisa dari, adadin da ya kai sahun gaba a nahiyar Afirka. (Mai fassara: Jamila)