Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Alhamis din nan cewa, kasar Sin tana bakin ciki matuka da yadda rikicin da ke faruwa a halin yanzu tsakanin Palasdinu da Isra’ila, ya haifar da hasarar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, tare da nuna matukar damuwa game da tabarbarewar yanayin tsaro da ma jin kai a yankin Falasdinu, ta kuma damu matuka game da mummunan tasirin da tashin hankalin zai haifar ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, kasar Sin ta lura cewa, kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta gudanar da taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kungiyar, inda ta zartas da wani kuduri dake goyon bayan kungiyar wajen taka muhimmiyar rawa kan batun Palasdinu.
- Shugaba Xi Ya Yi Rangadi A Biranen Jingdezhen Da Shangrao Na Lardin Jiangxi
- Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Yi Taro Kan Rikicin Isra’ila da Falasdinu
Kasar Sin da kasashen Larabawa na da kusan ra’ayi daya kan batun Falasdinu, inda bangarorin biyu suka yi kira da a hanzarta tsagaita bude wuta da kawo karshen hare-haren bama-bamai, da yin Allah wadai da ayyukan dake cutar da fararen hula, da kaucewa ta’azzarar al’amura da haddasa bala’in jin kai.
Wang Wenbin ya ce, kasar Sin tana son ci gaba da yin mu’amala da hadin gwiwa tare da dukkan bangarorin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, da sa kaimi ga yin shawarwarin zaman lafiya, da kokarin maido da shirin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya kan turba mai kyau.
Bugu da kari, a jiya manzon musamman na kasar Sin kan batun Gabas ta tsakiya Mr. Zhai Jun ya tattauna kan yanayin da Palestinu da Isra’ila ke ciki tare da mataimakiyar ministan harkokin wajen kasar Palestinu ta farko Amal Jadou ta wayar tarho, inda Zhai Jun ya bayyana cewa, kasar Sin ta damu matuka da rasuwar fararen hula da dama sakamakon rikicin Palestinu da Isra’ila.
Ya kara da cewa, yanzu abu mafi muhimmanci shi ne, a tsaigaita bude wuta nan take. Kuma kamata ya yi kasashen duniya su yi kokari domin sassauta rikicin, tare kuma da samar da taimakon jin kai ga al’ummar Palestinu. Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari domin cimma burin tsagaita bude wuta tsakanin sassan biyu, tare kuma da samar da tallafi domin sassauta rikicin jin kai, kana za ta ci gaba da shawo kan sassan biyu, su komawa shawarwarin wanzar da zaman lafiya, ta yadda za a daidaita batun Palestinu bisa adalci daga duk fannoni.
A na ta bangare, Jadou ta gode wa kasar Sin bisa matsayin adalcin da take kai game da batun Palestinu. A cewarta, Palestinu ta na da cikakken imani da kasar Sin, kuma tana fatan kasar Sin za ta ci gaba da taka rawar gani kan batun a halin da ake ciki yanzu. (Mai fassara: Ibrahim Yaya, Jamila Zhou)