Nada Mista Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi, hakan ya janyo cece-cekuce a ra’ayin wasu kwararru a Nijeriya.
A jiya ne dai, Tinubu ya nada Ola a matsayin sabon shugaban EFCC wanda zai shafe shekaru hudu kan kujerar EFCC, gabanin majalisar dattawa ta tabbatar da nadin nasa.
- Tinubu Ya Nada Olukoyede A Matsayin Sabon Shugaban EFCC
- Abubuwa 5 Game Da Sabon Shugaban EFCC, Ola Olukoyede
A cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa Ajuri Ngelale ya fitar, ta ce, Tinubu ya nada Olukoyede ne bayan da tsohon shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya yi ritaya a matsayin shugaban Hukumar.
Sai dai, wasu na tambaya kan halarcin nadin na Ola, musamman bisa la’akari da sashe na 2 (3) a cikin baka na dokar EFCC ta shekarar 2004 wadda ta nuna cewa, dole ne shugaban da za a nada a EFCC, ya kasance wanda yake kan bakin aiki ko kuma wanda ya yi ritaya a fannin tsaro na gwamnati ko ya kasance wanda ya taba yin aiki a wata hukumar tsaro, ya zama wanda yake da kwarewar aiki har ta tsawon shekaru 15.
Amma sai sanarwa Ngelale ta bayyana cewa, Tinubu ya nada Ola ne bisa karfin ikon da kudin tsarin mulkin Nijerya ya ba shi da kuma da yadda sashe na 2 (3) na dokar EFCC ta shekarar 2004 ta tanada.
Ngelale ya kara da cewa Ola, ya shafe sama da shekaru 22 yana aiki a matsayin kwararren lauya, inda ya ce, yana da kwarewa wajen tafiyar da ayyukan EFCC duba da ya taba rike mukamin shugaban ma’aikata a lokacin shugabancin tsohon shugaban EFCC Ibrahim Magu daga 2016 zuwa 2018 ya kuma taba rike mukamin sakataren Hukumar ta EFCC daga 2018 zuwa-2023 wanda hakan ya nuna cewa ya cancanci ya shugabanci EFCC.
Sai dai, an ruwaito Darakta a kungiyar Action Aid a Nijeriya, Andrew Mamedu, ya ce, Tinubu ya karya dokar da ta kafa Hukumar EFCC.
Shi kuwa wani kwararren lauya mai lambar kwarewa ta SAN, Victor Opara, ya ce, nadin ya yi daidai idan aka yi la’akari da sashi na 2 na dokar da ta kafa Hukumar ta EFCC.