Jiya Alhamis, an gabatar da rahoton “Nazarin da aka yi kan kudaden gudanar da ayyuka da kasar Sin ta baiwa kasashen Afirka” a yayin taron dandalin tattaunawar bunkasuwar kasashen duinya da aka gudanar a jami’ar Peking dake birnin Beijing na kasar Sin. Rahoton ya yi nazari kan ingancin tsarin samar da kudaden gudanar da ayyuka na kasar Sin a kasashen Afirka cikin shekaru 20 da suka gabata, inda ya bayyana cewa, kudaden da kasar Sin ta samarwa kasashen Afirka ba su kai kaso 10 bisa dari na bashinsu ba.
Rahoton na nuna cewa, tsakanin shekarar 2000 zuwa shekarar 2020, gaba daya, kasar Sin ta yi alkawarin samar wa kasashen Afirka taimakon kudi na dallar Amurka kimanin biliyan 160, kana, an samar da 90% daga cikinsu ga kasashe masu karancin kudin shiga da kasashe masu samun matsakaicin kudin shiga na nahiyar Afirka, domin ba da taimako gare su wajen neman ci gaba.
Haka kuma, rahoton ya bukaci a kara zuba jari ga kasashen Afirka, yayin da ya kafa tsarin samar da kudade ga kasashen Afirka mai inganci, domin taimaka wa kasashe masu karbar bashi wajen raya sana’o’in da suka dace da karfin su, da kara samun kudi ta hanyar fitar da kayayyaki, ta yadda za a kara karfin kasashen a fannin biyan basussuka. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)