Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa daku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya.
Ga abubuwan da uwargida za ta tanada:
Zuma, lemon tsami, kwai:
Ga kuma yadda za ki hada:
Da farko za ki fasa kwanki sai ki zuba farin a cikin wani dan kwano haka, farin kadai ban da mununuwar, kwai guda daya ma ya wadatar wani zubin ma sai ki ga dayan ya yi yawa daganan saki kawo lemon tsami shima rabin lemon ya isa ba sai kin gasa shi gaba daya ba ki dai saka kamar misali cokalin shayi guda daya zuwa daya da rabi ya wadatar. Idan kika matse shi sannan sai zuma shima ki sa kamar cokalin shayi daya zuwa daya da rabi ya isa daga nan sai ki hada su waje daya ki yi ta kadawa yadda sai sun hadu sosai sun gauraye yadda kowanne zai zama ya gaurayu a ciki sannan ki dauraye fuskarki da ruwa dumi ki shafa fuskaki da shi amma ban da zagayen idonki, gaba daya dai fuskaki ki barshi ya bushe ya yi kamar minti goma sha biyar haka sai ki wanke fuskarki da ruwan dumi.
A misali uwargida idan za ki yi kamar sau daya a sati in sha Allahu za ki ga canji sosai fuskarki za ta yi kyau ta yi laushi santsi duk wani tabo za ki ga ya fita. Sannan idan fuskarki tana yawan bushewa za ki iyayin sau biyu a sati, za ki ga canji sosai in Allah ya yarda.
Gawani hadi idan kina ganin misali baki da kayan wancan hadin gaba daya:
Shi wannan hadi kwai kadai ake bukata sai tushu fefa. Yadda za ki yi za ki fasa kwain sai ki zuba farin ban da kaunduwar a cikin kwano in kina da neskof za ki iya dan sawa amma kadan yatsanki guda biyu za ki sa ki dan bincina sai ki dan zuba a cikin kwain sai ki dan kada shi za ki ga kalarsa ta dan canja kadan haka idan kuma baki da neskef din kwan kadai ma ya wadatar bayan kin kada shi a kwano haka kin dan buga shi sai ki shafe fuskarki da shi idan kika shafe fuskarki da shi sai ki samu tushu ki mammanna a kai yadda idonki ba za ki rufe shi haka hancinki ma da bakinki amma ya zamana ko ina ya samu ruwan kwain ki tabbatar kin yi shi ko ina, bayan kin mammanna tushu din sai ki dauki ragowar ruwan kwain sai ki sake shafawa a saman tushu din ki bishi yadda gaba daya kin rufe tushu din yadda tushun zai jiku yadda har kan fatarki ma za ki jiyo ruwan kwan ban da wanda yake kan fatarki.
Bayan kin gama yin haka sai ki bar fuska ba yawan motsi ko wani dariya wanda zai canja yanayin fuskar ya zamana haka za a barshi ya bushe, idan ya bushe haka za ki daye wannan tushu din daga kasa ba daga sama ba ya zamana wato wajen haba za ki fara jan sa a hankali har ki fitar da shi gaba daya. Idan kina yi shima koda sau daya ne a sati ko sati biyu shima in sha Allahu za ki ga canji.