A jiya ne, aka gudanar da taron karawa juna sani kan bikin cika shekara daya da kaddamar da shirin Leaders Talk na babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG a nan birnin Beijing. Shugaban CMG Shen Haixiong ya jagoranci taron, inda ya tattauna da wakilan hukumomin kwamitin tsakiya na JKS da gwamnatin kasar, da masana da kuma tawagar tsara shirin, don ba da sabbin ra’ayoyi kan kyautata shirin.
Shirin Leaders Talk ya sami cikakkiyar damar yin amfani da harsuna guda 68, tashoshi 191 dake kasashen waje, da kuma gidajen talibijin da rediyo da sabbin hanyoyin sadarwa na CMG, ta yadda ake iya kama shirin cikin harsuna da ma hanyoyi daban daban.
Tun lokacin da aka fara gabatar da shirin, jimilar mutanen da suka kalla ko saurari shirin, ta kai biliyan 10, kuma yawan masu kallo ko masu sauraron shirin ta dukkanin hanyoyin sadarwa ya kai miliyan 508.(Safiyah Ma)