A shekarar 1517 Katolik Bishop,Bartolome de las Casas ya yi wani rubutu inda ya bada shawara dangane da amfani da bayi daga nahiyarAfirka saboda kamar yadda ya ce ‘yan Afirka suna da nagarta da karfi ba kuma za su iya tada wata kura ba,babban al’amari kuma shi ne irin cututtukan da fararen fata Turawa suke fama da su, suma hakanan sun saba da su.
Zai yi wuya su kamu da wata cuta bare har ayi tunanin su mutu, saia aka yi sa’a domin kuwa shawarar da Bishop de las Casas’ ya bada aka amince da ita sai aka fara farautar su a matsayin in kama a sayar da su a matsayin kaya.
- Cinikin Waje Na Kasar Sin Yana Inganta
- ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Tara Min Kudi Don Yi Wa Tinubu Waka Saboda Kaunarsa -Mawaki Rarara
Bada dadewa ba sai sauran kasashen yammacin Turai suka fara shiga ala’amarin a Amurka koda ya ke dai duk al’amarin daya ne sika shiga ciki gadan-gadan kamar yadda kasar Fotugal ta yi, suka dauki mataki na samo bayai daga nahiyarAfirka suna kuma samun masu saye a duk lokacin da suka kawo wa masu sayen.
Da yake su Turawan masu son sayen bayin ba kowanne daga cikin bane za su iya barin inda suke ba su je nahiyar Afirka saboda gudun kada su hadu da sauro don gudun kamuwa da cuta,shi ya sa bukatar ‘yan wasu mutane daga Afirka da za su taimaka wajen samo masu bayi.Irin wannan rayuwar da suka yi ta farautar bayi ta yi kama da halin da ake fuskanta na garkuwa da jama’a.
Da yake kasar Birtaniya a wancan lokacin ita ce ta kasance tamkar wata jagorancin duniya domin kuwa kasar ce ta mamaye al’amarin cinikin bayi a lokacin har ya zuwa shekara 300, me yasa abin ya fara ne daga yaki wajen amfani da makami zuwa inda aka maida akalar al’amarin zuwa tattalin arziki?
Duk wani alhakin cinikin bayi an dora shi ne kan dan kasar Birtaniya mai suna John Hawkins, Hawkins shi ne wanda ya maida ”sana’ar ta zama ta zamani” daga yadda su Turawan Fotugal suka fara ta yadda ake yin abin ba sani ba sabo zuwa wadda ake ganin akwai kasuwanci ne mai mutunci ”Daga nan sai jiragen ruwa suka fara tasowa daga Ingila dauke da bindigogi,madubai,da giyasai dai jiragen suna zuwa wani wuri ne da ya zama tashar cinikin bayi inda yanzu ake kiran wurin da suna Niger Delta. Daganan kuma sai ‘yan kasa su dauki bindigoginsu da giya inda su kuma za su basu mutane a matsayin bayi; sai aka fara tafiya da bayin zuwa wurin da basu taba zuwa ba a ratsa ta ruwa,idan an isa wurin da aka yi niyyar zuwa su bayanin ana yin bani gishiri ne in baka manda inda ake bada sikari,Auduga,da kuma kudi.
Wadannan kauan za a sake maida su zuwa yammacinTurai saboda a samu riba mai yawa, idan aka yi la’akari da yadda ake son giya da makamai a Afirka,shi ya sa bayi a kasar Amurka suke wni abinda zai kawo kudi wannan wani abu ne da ya shafi kasuwanci.
Tun farko dai mutanen da ake bayar da su a matsayin bayi ana samun sune sanadiyar yaki, ko kai hari/ da mamaya a wani abu da ake kira, efulefu.Sai dai kuma da bukatar karun bayin ta taso sai a aka kara kaimi na yake- yake da kai hare- hare ba domin komai ba sai saboda a cimma burin na kasuwancin bayin hakan ta kasance saboda an samu bukata ta sikari da auduga mai arha a yammacin Turai
Ana cikin haka sai aka samu wani matashin mutumin kasar Birtaniya wanda ya shugabanci wata akida ta rashin son ci gaba da cikin bayi inda kuma ya yi sa’a ana kiran shi da suna William Wilberforce.
Wani abin mamaki lokacin da Turawan Ingila suka kafa dokar hana cinikin bayi a shekarar 1807 kasashen Fotugal, Sifaniya, Faransa,da Amurka, abin ya yi matukar bata masu rai
Lokacin da Turawan Ingila suka hana cinikin bayai a shekarar 1807 sai da Sarkin Ashante ya rubutawa Sarkin Ingila wasika yana cewa me zai sa su yi masu haka,ba shi kadai bama har da Oba of Benin,da sun nuna basu dadin hana cinikin bayai ba.
Kamar Sifaniya da Fotugal yadda aka yi bayani sai dai kuma an koma yin cinikin bayain ta barauniyar hanya.An yi kokarin karya dokar kamar a shekarar 1840 sai dai abin ya cimma nasara ba.