Sama da kasashe 60 ne suka tabbatar da halartar baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na kasa da kasa karo na shida ko CIIE a takaice, wanda aka shirya gudanarwa daga ranar 5 zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba, a cewar hukumomi.
Baje kolin kasar wani muhimmin bangare ne na CIIE kuma ana sa ran kowace kasa da e halarta za ta baje kolin sabbin fasahohi, masana’antu masu karfi da yanayin zuba jari. Rumfunan kasa da kasa na bana za su hada da kasashe masu tasowa, tun daga masu karamin karfi zuwa masu ci gaba.
Ya zuwa yanzu, sama da kamfanoni 3,000 daga kasashe sama da 120 ne suka tabbatar da halartarsu, kuma girman yankin baje kolin zai wuce murabba’in mita 360,000. (Muhammed Yahaya)