Hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta yi juyayin mutuwar wata matashiya Joel Grace Chalya KD/23A/4386, wacce aka kashe da safiyar ranar Laraba a Kaduna.
LEADERSHIP ta bada rahoton cewa wasu ‘yan daba ne suka daba wa marigayiyar wuka tare da kwace mata waya a Barnawa GRA da ke Kaduna, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarta.
- CMG Ya Daddale Takardun Hadin Gwiwa 10 Da Kasashe 9
- Motar Gidan Yari Ta Afka Kan ‘Yan Kasuwa A Kwara
Abokan marigayiyar sun yi gaggawar sanar da hukumar NYSC, inda ita kuma hukumar ta yi gaggawar kai ta asibitin Harmony da ke Barnawa har ma ta fara farfadowa daga jinyarta amma daga bisani rai ya yi halinsa.
NYSC a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Eddy Megwa, daraktan yada labarai na hukumar, ta nuna damuwarta kan lamarin tare da mika ta’aziyyarta ga iyalan mamaciyar.
Sanarwar ta ce, “Muna kan aikin hadin guiwa da hukumomin tsaro domin tabbatar da an hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan aikin.
“Muna kira ga jama’a da su yi aikin hadin guiwa da jami’an tsaro domin tabbatar da dukkanin masu hidimar kasar da aka tura yankunansu sun samu cikakken kariya domin bada tasu gudunmawar wajen ci gaban kasa”.
Ta kara da cewa, “Matasa masu yi wa kasa hidima ‘ya’yanmu ne, ‘yan uwanmu ne, kannenmu ne, dole ne mu hada kai da dukkanin ‘yan kasa mu kare su.”