Hukumar hana fasa gwabri ta kasa wato Kwastam (NCS) ta ce, rungumar aiki da fasaha za ta kawo ingantuwar gudanar da harkokin kasuwanci gami da karin samun kudaden shiga a kasar nan.
Da yake jawabi a wajen wani taron kwastam na duniya (WCO) kan fasaha da baje kolin basira, mai rikon kwanturola janar na hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, wanda ya yi imanin cewa rungumar wadannan hanyoyin na fasaha za su kawo gagarumin sauyi a Nijeriya, ya bayyana aniyarsa ta bullo da tsare-tsaren da za a rungumi bangaren hannu biyu-biyu a Nijeriya.
- An Kambama Marubutan Kasar Sin A Babban Bikin Ba Da Lambobin Yabo Na Hugo
- Mun Damu Kan Bayyanar Mayakan Kungiyar Ansaru A Yankinmu — Mutanen Birnin Gwari
LEADERSHIP ta labarto cewa taron na da manufar zaburar da mahalarta da su rungumi fasaha a matsayin wani mataki da zai kai ga shawo kan kalubalen da aikin hukumar Kwastam ke fuskanta.
Tawagar Nijeriya da ke karkashin jagorancin Adeniyi ne suka halarci babban taron da aka gudanar a Ha-noi, Bietnam, ya ci gaba da cewa, “Mun koyi abubuwa da daman gaske, yadda ake tura bayanan sirri, koyon amfani da na’ura, da kuma bangarorin nazari daban-daban da za su kai ga shawo kan matsaloli da dama na bangaren ayyukan Kwastam da kuma lalubo bakin mafita.”
Shugaban kwastam din ya nuna muhimmancin taron WCO kan fasahar, wanda ya nuna hakan a matsayin mataki babba na kyautata aiki ga kwastam, kamfanonin jere, masu daukan nauyi, kamfanonin fasaha, da samun karin hadin kai wajen inganta aiki, musayar fahimta a bangaren fasaha da ya shafi ayyukan kwastam.
Ita ma mataimakiyar kwanturola janar a bangaren ICT, ACD Kikelomo Adeola, wacce tana daga cikin wadanda suka halarci taron, ta bayyana kwarin guiwarta na rungumar tsarin kasuwanci ta yanar gizo. Ta jaddada muhimmancin tsarin da fasaha wajen inganta ayyukan kwastam.