Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanar da cewa, tsakanin watan Janairu da na Satumban bana, an kafa sabbin kamfanoni masu jarin kerare har 3,7814 a kasar, adadin da ya karu da kashi 32.4% bisa na makamancin lokaci na bara. Inda kasar ta samu damar yin amfani da jarin waje da yawansa ya kai Yuan biliyan 919.97, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 125.74.
Idan an duba karuwar da aka samu a sana’o’i daban daban, za a ga jarin waje da bangaren masana’antun kere-kere ya samu ya karu da kashi 2.4%. Cikinsa, aikin sarrafa kayayyaki bisa fasahohin zamani masu inganci ya samu karin jarin waje, inda karuwar sa ta kai kashi 12.8%. (Bello Wang)