A ƙoƙarin ta daukaka darajar ilmi, Gwamnatin Jihar Kano ta zaɓi ɗalibai 1001 da ta fara ɗaukar nauyin karatunsu a digiri na biyu a ƙasashen waje.
An rahoto cewa, daga cikin Daliban akwai wadanda aka tura zuwa Jami’o’in kasar Indiya wasu kuma zuwa Jami’o’in Kasar Uganda domin samun ilimi a fanni daban-daban.
- Dage Takunkumin CBN A Asusun Ajiyar Wasu Mutane Da Kamfanoni Ya Haifar Da Da Mai Ido
- Zaben 2023: Takaddamar Kashi 94 Cikin 100 Na Kujerun Da Aka Lashe Ta Dora Shakku Kan INEC
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya rage kuɗin rajistar shiga jami’a da na zangon karatu da kashi 50 bisa 100 a kwanan baya, ya ƙaddamar da Shirin Bada Tallafin Karatu a Ƙasashen Waje, wanda aka fara ranar Alhamis da jigilar ɗalibai 550 daga Kano.
Gwamna Kabir ya ce, ya ɗora wannan gagarimin aikin alheri ne daga inda tsohon Gwamnan Kano, kuma madugun Kwankwasiyya, Rabi’u Kwankwaso ya tsaya, a lokacin mulkinsa.
Ya ce ayyukan alherin da gwamnatin Kwankwaso ta yi wa al’ummar Kano a baya, su na da muhimmancin da ba za a iya daina ci gaba da su ba.
Kabir ya ce, ga shi nan ƙarara ana ta cin moriya da amfanar waɗanda suka je waje karatu a ƙarƙashin gwamnatin Kwankwaso, inda wasu na riƙe da muƙamai sosai a gwamnati da sauran fannonin ayyukan yau da kullum.
Ya lissafa wasu da suka haɗa da Kwamishinan Ilmi Mai Zurfi, Dakta Yusuf Ibrahim, Shugaban Sashen Ƙididdigar Alƙaluma na Jihar Kano, Farfesa Aliyu Isa Aliyu da Mashawarci na Musamman a Fannin Ƙirƙire-ƙirƙire, Dakta Bashir Muzakkir da sauran su.
Gwamnan ya ce, “Bari na bayyana cewa, shi wannan shirin tallafin gurbin karatun waje, madugun mu Sanata Rabi’u Kwankwaso ne ya ƙirƙiro shi.”
Ya ce Kwankwaso sai da ya ɗauki nauyin rukuni-rukunin ɗalibai har rukuni uku zuwa ƙasashe 16 daban-daban.
“Wannan ƙoƙari ya sa an samu nasarar samar da daktoci, masu digiri na biyu da dubban ƙwararrun likitoci, injiniyoyi, matuƙa jirgin sama da gwanayen ayyukan harkokin jiragen ruwa da sauran su.
A jawabin sa tun da farko, Kwankwaso ya gode wa wannan gwamnati ta Abba Kabir, ganin yadda ta ci gaba da ayyukan alherin da ya fara a lokacin ya na Gwamnan Kano.
Ya ja kunnen ɗaliban su kasance masu ɗa’a kuma jakadun Kano da Nijeriya nagari a duk inda suka samu kan su.
Ɗaliban da dama sun gode wa Gwamnatin Kano, Gwamna Abba da kuma Kwankwaso.
Kafin tashinsu sai da Gwamna Abba Kabir ya damƙa wa kowa kuɗaɗen alawus ɗin sa na daloli a hannu, aka kira su taron dina a Gidan Gwamnati, sannan kuma Gwamna da Kwankwaso suka raka su har cikin jirgi.
Abba da Kwankwaso ba su bar filin jirgin Malam Aminu Kano ba, sai da suka ga tashin jirgin da ya ɗauki ɗaliban.