Wakilin kasar Sin na musamman kan al’amuran yankin gabas ta tsakiya Zhai Jun ya yi kira a jiya Asabar yayin taron kolin da aka gudanar a birnin Alkahira kan rikicin Falasdinu da Isra’ila cewa, a dakatar da ayyukan soji wanda ke kara tsananta halin da ake ciki a zirin Gaza, da kuma bude hanyoyin ba da agaji jin kai.
Zhai ya bayyana matukar bikin cikin kasar Sin kan yadda fararen hula ke mutuwa, da kuma mummunan yanayi da ake ciki na jin kai sakamakon barkewar rikicin. Zhai ya kara da cewa kasar Sin tana adawa da kuma yin tir da duk wasu ayyukan da ke cutar da fararen hula da ma duk wani nau’in aiki na keta dokokin kasa da kasa.
Ya jaddada cewa ci gaba da ruruwar rikicin Falasdinu da Isra’ila, ya sake tabbatar da cewa ba za a yi watsi da ko a manta da batun Falasdinu ba. Babbar hanyar warware rikicin Falasdinu da Isra’ila da aka dade ana yi shi ne aiwatar da shirin “samar da kasashe biyu” da kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta, ta yadda za a tabbatar da zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra’ila.
Ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin aiki tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa, da sauran kasashen duniya, wajen warware rikicin cikin sauri, da nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu wajen maido da halastaccen hakkinsu, da aiwatar da shirin “samar da kasashe biyu” da kuma sa kaimi ga samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya. (Yahaya)